SHEIKH DAHIRU USMAN BAUCHI shi ne mataimakin shugaban kwamitin koli na kungiyar malaman da ke bayar da fatawa, kuma fitaccen malamin addinin Islama, jigo a Darikar Tijjaniyya a Afrika. Bayan haka dattijo ne wanda a wannan wata na shekarar Musulunci Almuharram ya cika shekara 99 a duniya. A makon da ya gabata ya fito ya nemi gafarar duk wanda ya saba masa kuma shi ma ya ce ya yafe wa kowa, kana ya nuna cewa Allah ya cika masa burinsa a rayuwa illa abu guda daya da ya rage. Wasu ‘yan jarida ciki har da wakilinmu KHALID IDRIS DOYA sun tattauna da daya daga cikin ‘ya’yansa da ke ja masa baki, GWANI SAYYADI ALIYU SISE DAHIRU BAUCHI domin jin karin bayani. Ga hirar:
A makon jiya kun yi walimar karrama daliban Alkur’ani masu karatu da kira’o’i tare da malamai, mene ne hikimar hakan?
Alhamdu lilahi abin da ya jawo muka yi wannan bikin karrama daliban Maulana Sheikh Dahiru Usman Bauchi da suka haddace Alkur’ani kuma suke kokarin kwarewa cikin ilimin kira’o’i daban-daban na Alkur’ani da kiyayeshi shi ne, Shehi ne ya ba mu umurnin mu yi haka, saboda yadda yake kulawa da Alkur’ani da tilawarta da karantata da kuma kula da yadda ake koyon ilimin Alkur’ani, ya sa a kowani lokaci da lokacin da yake da karfinsa da kansa yake tafiya yake bibiyar yaya karatun yake. Yanzu ma ya na saurara wani lokaci ya kan yi karatun tare da daliban. Akwai kuma dalibansa da yake ya yi tafiya yana Abuja suka nuna gwaninta wajen tilawar Alkur’ani da karantata da haddaceta da Kira’o’i kuma kowani yaro cikin almajiransa in zai yi karatu zai fara fada maka irin kira’ar da zai yi warshu ko hafsu ko wani iri dai, zai fada kafin ya karantawa.
Shehi sai ya ji karatunsu da yawa haka abin ya yi masa dadi ya yi addu’o’i masu yawa ya roki Allah ya saka wa duk wanda ya taimaka masa ya tsaya masa tafiyarsa ta kai haka da alheri. Kuma Shehi ya ce tun lokacin da aka yi masa abin da aka yi masa a Kaduna, ba ya jin dadi domin ya ga wadansu sun taso kan sai sun hana karatun Alkur’ani. Amma da abin da ya gani ya san cewa Alkur’ani ya na nan Allah yana cigaba da kiyaye abin sa, saboda kowa ya ji tilawar wadannan Almajirai nasa lalle zai san cewa su na kokari sosai wajen kiyaye Alkur’anin.
Saboda haka ne Shehi ya bada umurni cewa in mun dawo gida mu kira taro mu karrama wadannan dalibai, a matsayin wani mataki na karfafa musu guiwa. Bayan su kuma akwai daga cikin Malamanmu akwai bakin Larabawa daga kasar Misira wadanda su ma Malamai ne da ke karantar da Alkur’ani su biyu, daya daga cikinsu ya kammala zamansa na shekaru uku, daya kuma zai tafi hutu, da kuma Malaminmu Alaramma Salihu Gano su ma dukka Shehin ya ce a karramasu. Ba su kadai ba duk wanda ya zo wannan wurin ma Shehi ya karramashi da littafin da ya fi kowani littafi shi ne ya ba shi Izu 60 na Alkur’ani, su kuma wadanda suka yi karatun karramawarsu daban ne da malamansu.
Me ya banbanta irin tarbiyyar da Shehi yake bai wa Almajiransa da na sauran malamai?
Wannan tambaya tana dawuyar amsawa saboda ladabi, amma in za ka dunkule tarbiyyar Shehi da yake wa Almajiransa da ‘ya’yansa shi ne ba kamar koyi da sunnar Manzon Allah, kamar kulawa da tilawar Alkur’ani da karantashi da haddaceshi, kulawa da zikirin da istigfari da Salatin Annabi, gujewa duniya da neman lahira. Wato Shehi ya hori Almajiransa da neman lahira fiye da neman duniya kuma shi da kansa ya tsaya musu kan haka. Kuma Shehi mutum ne da ya zama jagora na zaman lafiya a Nijeriya, saboda ya koyar da almajiransa da ‘ya’yansa su zauna lafiya da kowa kuma a kullum duk lokacin da Shehi zai yi wani abu sai ya yi addu’a ya roki Allah ya ba mu lafiya da zama lafiya da kwanciyar hankali a Nijeriya.
Ka ga wannan irin addu’a ba mu ga mai yinta ba dare ba rana a kowani lokaci kamar Maulana Sheikh ba; shi jigo ne na zama lafiya, yanzu ka kwatanta ko ka gwada Almajiransa da wadanda suke sukan tafiyarsa ka gani, su wanene suke tsaye kan karatun Alkur’ani da haddaceshi, su wanene suke tsaye kan kiyaye Alkur’ani da karantashi da tilawarsa, su wanene kuma suka fi mallakar abin duniya, in ka duba za ka ga bangaren Shehi su ne masu kokari da himma wajen koyi da sunnar Manzon Allah fiye da kowani bangare da ke sukar tafiyarsa. Amma mun sallama wancan bangaren sun fi mu samun abin duniya. Misali in ka daukeni ni da nake jaa masa baki ba wani abu da na mallaka a rayuwata sai fili guda daya, shi ma bai wuce na miliyan daya da dubu biyu ba, sai mota guda daya ita ma ta mutu, ba ni da wani ajiyayyen abu a banki ina da iyalai da yawa mata hudu, kuyanga daya da ‘ya’ya 37.
Amma Shehi ne a tsaye a kaina da sauran ‘yan uwana mu je mu yi wa addinin Allah aiki, kuma har yanzu shi muke yi, ka ga ba za mu yi daidai da bangaren da su in ka dubi sunarsu da irin abin duniya da suka tara ba. Mu kuwa bamu da komai sai Alkur’ani da Zikirin Allah.
Kuma har yanzu ka kwatanta a bara gwamnonin Arewa sun yunkuro wai sun hana Bara. Sai Gwamnan Kaduna na wancan lokaci ya tura jami’an tsaro gidan Shehi a Kaduna, ya kwashe almajirai masu karatun Alkur’ani cikin dare ya tafi da su, in ka kwatanta da yawan magoya bayan Shehi a ciki da wajen kasar nan, in ba mai son zama lafiya ba ne da an yi tashin hankali a kasar nan kuma wannan shi ne ma abin da ya fi dadada masa rai, bai ji dadi ba sai da wadannan almajirai suka je suka yi ta rokonsa su na masa karatun Alkur’ani da kira’o’i har ya ji dadi ya yafe. Ka ga wannan zalunci ko Shehi ba babban Malami ba ne, talaka ma in za ka shi ga gidansa sai ka nemi ilimi da izini, amma haka aka yi, sa’a saboda kaunar da yake yi wa zama lafiya ba a yi wani tashin hankali ba.
Kai ne Shehi ya turo da sako da muryarsa yake shaida wa al’umma cewa Allah ya cika masa burinsa gabaki daya saura abu daya tak mene ne wannan abun?
Alhamdu lillahi jin dadin karatun da wadannan dalibai nasa na Kira’at da suka yi, suke kokarin kiyaye Alkur’ani ga karatu ga Tajwidi ga himma ga su kanana yara ya sa Shehi ya ji dadi cewa an samu masu kula da karatun Alkur’ani da kiyayeshi saboda haka, umurni na farko da ya bayar shi ne ya hori dukkan Almajiransa da su kiyaye Alkur’ani su rike Alkur’ani in sun rikeshi sun rike gaskiya kuma su na tare da Allah ba za su tabe ba. Sai ya roki ga fara musulmin duniya baki daya da duk wani dan adam da in ya masa wani abu da bai ji dadi ba ya yafe masa, shi ma in wani ya masa wani abu ya yafe masa. Ya ce Allah ya cika masa burinsa, saura abu daya shi ma yana rokon Allah ya masa shi ne cikawa da Imani.
Shehi ya ba banban da wasu malamai wajen bayar da fatawa shin akwai wadanda ba su amince da fatawarsa ba?
A duk duniyar Musulunci ba wadanda ba su bi karantarwar Sheikh ba sai wadanda suke su Almajiran su ibn Taimiyya ne, da Wahabiyawa, amma bisa misalan da na baku dazu inda a ce zaka kwatatanta tsakaninsu, ka duba irin renon da Shehi ya bai wa ‘ya’yansa da Almajiransa, ka kuma duba su wadanda suka ba ‘ya’yansu, za ka ga bangaren Shehi ne ke kula da Ilimi da Sunnar Manzon Allah Zikiri da karatun Alkur’ani. Ka dauki misali ni a cikin kananan Almajiran Shehi, ni nake Ja masa baki na haddace Alkur’ani a hannunsa, na yi imomi na sanin dukkanin ruwayoyin Kira’o’in Alkurani, don Allah Almajiran wadancan su ga mutun guda suka rena suka kera shi kamana, mu gwada da su a ga ni, in kuma aka gwada aka rasa ashe ka ga ba su da gaskiya ke nan saboda irina ma karami cikin Almajiran Shehi sun kasa kawo kamarsa. Don haka kar su sake cewa komai kan harkokin musulunci, saboda su ba su yi karatun da za su zama malamai ba tukunna, karsu sake zagin Shehu Tijjani, ko Shehu Ibrahim, ko shi Maulana Sheikh Dahiru Bauchi. Kuma su zo mu yi zube da almajiransu da namu a yi karatu saboda Allah za ka ga inda karatu yake da inda neman duniya ne ya fi tasiri.
A matsayinka na Darakta da ke kula da harkokin Ilimi ko yaya fasalin Makarantunku na karatun Alkur’ani suke a yau?
Alhamdulillahi gaskiya kidddigan makarantu na Maulana Sheikh ya na dawuya ba iya tantacesu saboda wadansu, ba mu iya sasu a lissafi ba saboda tun ba a haifemu ba yake kafa tsangayu yana karantarwa a wurare daban-daban, kuma kullum adadinsu hauhawa ya ke yi a gida Nijeriya da kasashen waje. Misali a wani kididdiga da muka yi kwanakin baya, a karkashin gidauniyar Maulana Sheikh Dahiru Bauchi mun bude makarantu 557, muna da Malamai 1,973, dalibai 948,552, daga cikinsu akwai mahaddata wadanda suka hadddace Alkur’ani su 20,271, kuma mun gina azuzuwa 1,625, wadannan a cikin gida Nijeriya ne, a kasashen da ke Makwabtaka da Nijeriya kuwa misali a kasar Nijar Shehi ya bude makarantu guda shida da Malamai guda 16 da dalibai 1,261, daga cikinsu dalibai 92 ne suka haddace Alkur’ani, mun kuma gina azuzuwa guda 15. A Jumhuriyar Benin ma mun bude makarantu tara mun gina azuzuwa 26, akwai dalibai 1,110 su na kokarin haddace Alkur’ani, amma a kasar Kamaru kuwa mun bude makarantu guda biyar, muna da azuzuwa guda 16, da Malamai guda biyar muna da dalibai 638 daga cikinsu guda hudu sun haddace Alkur’ani, ka ga wannan adadin, adadi ne na wadanda muka bude karkashin Mu’assasa amma aikin Shehi Allah ne kawai ya sani.
Kuma wani abin mamaki yadda yake matsawa Almajiransa su rike Alkur’ani haka kuma yake matsawa ‘ya’yansa su rike Alkur’ani da zikirin Allah. Ka ga a yau Shehi yana da ‘ya’ya na cikinsa mu 76 dukkanmu Mahaddata Alkur’ani ne. Haka kuma Jikokin Shehi yau sun kai 99 dari ba daya ke nan duk sun haddace Alkur’ani sannan yanzu an samu Tattaba kunne wato ‘ya’yan Jikokin guda biyu da su ma Allah ya basu Tilawar Alkur’ani, koda wannan kokari ka kwatanta za ka ga cewa akwai banbanci tsakanin tarbiyyan Shehin da masu sukar tafiyarsa don ban yi tsammani masu sukan tafiyarsa za iya kawo maka wannan kididdiga ba.
Wasu shawarori ko sako kake da shi ga al’ummar Musulmai?
Shawarar dai kamar kullum bai wuce a duba irin abin da Waliyyan nan suke ba mu na tarbiyya ba, a kula da su a rikesu da kyau. In an rikesu da kyau za a samu babban rabo a lahira. Kuma a guji zage-zage da sukar Waliyyai da manyan bayin Allah, domin yin haka yana haifar da fushin Allah madaukakin Sarki. Kullum Shehi ya na jan hankalinmu kan cewa Allah ya ce “Duk wanda ya yi gaba Waliyyina na umurceshi ya fito mu yi yaki da shi”. Wadannan bala’o’i na tsadar kaya da sauransu da ke damunmu a dubiya duk saboda zagi waliyyan ne ya jawo, kuma ko baka san waliyyan ba ka san musuluncin da yake hannunka a yau su ne suka bada gudummawa ya iso gareka. Ya kamata a yi kokari a hada kai a guji bata mutuncin juna a yawaita Istigfari domin Allah ya sawake mana wadannan masifu da wawayen cikinmu suka jawo mana. Mu yi ta addu’ae Allah ya ba mu lafiya da zama lafiya da kwanciyar hankali a Nijeriya, Allah kuma ya kara bayyana gaskiya ya nuna wa mutane inda hasken musulunci yake.
Na biyu muna rokon sabon shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, da ya karrama mutane biyu saboda su ma son Almajirai na daya tsohon Gwamnan Bauchi Mallam Isa Yuguda ya nada shi mukamin Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN) saboda a lokacin da yake gwamna ya taimaki Almajirai kowani wata miliyan 55 yake bai wa Almajirai mutum dubu goma sha daya da motoci fiye da 20. Na biyu kuma Gwamnan Jihar Yobe Mai Mala Buni ya kamata Tinubu ya karramashi cikin gwamnonin Arewa saboda shi ne Gwamnan da ya zo ya bai wa Shehi hakuri lokacin da Nasiru El-Rufai ya kwashe masa almajirai, kuma Mai Mala ne kawai ya fito fili ya ce Almajirai su dawo a Jiharsa.
Babban sako na shi ne, kuma a yanzu muna so gabaki dayanmu mu rike wannan wasiyya da Shehi ya mana na cewa mu kula da Alkur’ani, mu rike Alkur’ani in mun rikeshi mun rike gaskiya kuma ba za mu wofinta ba. Mun ji wannan fada zamu kara daukan matakai na kara riko da Alkur’ani kamar yadda ya umurcemu.