Mai karatu, MALAMA FATIMA ZAHRA ZAMSARF faitacciyar Marubuciya ce da tauraruwarta ke haskawa a ‘Social Media’ Musamman Facebook.Rubutunta akwai ilimi, basira da hazaka a ciki.
Ta rubuta littattafai kusan guda hudu, ciki akwai “Biyayya”, “Sanadin Mijina”, “Mafarikin Nisa A Rayuwa”, da kuma ” Abokai” sai dai duk labarin soyayya ne da gwagwarmayar rayuwa. Wakilinmu YUSUF KABIR ya yi hira da ita, ga yadda hirar ta kasance:
- ‘Yan Takarar Jihar Kano Sun Gamsu Da Taron KJPF
- Ranar Malaman Kasar Sin: Menene Sirrin Ci Gaban Kasar Sin?
Wacece Zahra Zamsarf
Suna na Fatima Abdurrazak wacce aka fi sani da Zarah A. Zamsarf. Ni haifaffiyar garin Katsina ce.
Batun karatu fa?
Na yi karatun Firamare da Sakandare duka a Katsina, inda na kammala a shekarar 2019, amma ban cigaba da wata makaranta ba har yanzu, ina dai kan nema inshaAllah. Karatun addini ma Alhamdulillah na yi karatu nane a gida tare da taimakon mahaifina.
Yaushe kika fara rubutu?
To idan dai nace ga lokacinb da na fara rubutu gaskiya na yi karya, zan iya cewa an haifeni da abin ne, saboda tun ina Firamare nike rubutu, ina rubuta labarai irin na tatsuniya haka, bayan na kammala primary kuma sai yanayin rubutuna ya fara canzawa.
Zuwa yanzu kin rubuta Littafai guda nawa?
Alhamdulillah, inada littattafai a kasa kusan guda hudu, Akwai ” Biyayya”, ” sanadin mijina”, ” mafarikin Nisa a rayuwa”, da kuma ” Abokai” sai dai duk labarin soyayya ne da gwagwarmayar rayuwa, amma har yanzu ban taba buga ko daya ba. Kuma a social media ma nakan saka amma ba sosai ba gaskiya.
Wadanne Marubuta suka fi jan hankalin ki?
Gaskiya marubutan da suka fi karkata alkalaminsu a kan zamantakewa da soyayya su suka fi jan hankalina, kuma irin su suna da yawa sosan gaske, amma a cikinsu akwai mahaifiyata, ta yi mani tasiri fiye da tunanin mai tunani, zan iya cewa ita ce tauraruwata ma gaba daya. Littattafan da suka mani tasiri gaskiya suma suna da yawa sosai. Akwai kamar “Men are from Mars women are from benues”, “Create or hate” da dai sauransu da yawa.
Kina yawan rubutu a kan zamantakewar aure mi ya sa hakan?
To da yake dai lamarin zamantakewar aure lamari mai girman gaske, gaskiya na fahinci da yawan mutane sun jahilci meye zamantakewa din, shi yasa na zabi wannan bangaren domin ba da gudummawa, duk da shi ilimi kogi ne, yawan yadda kake ganin kasan abu yawan yadda baka sanshi ba din. Amma tabbas na zabi nan ne saboda karancin sani, da rikon wasa da mutane ke yi wa auren.
Mene ne babban burinki a duniyar rubutu?
Buri na shi ne ace sakon da nake kokarin isarwa yana isa, ina fatan a samu sauyi daga yadda ake yanzu din, kuma ina fatan na wuce haka, alkalamina ya zama kowane bangare yake tabawa, ba iya zamantakewa da soyayya ba.
Ya kike ganin amfanin ‘Social Media’ ga marubuci?
Tabbas tanada gayar muhimmanci ga marubuta, saboda ‘social media’ a yanzu ita ce hanya mafi sauki wurin isar da sakon marubuci (musamman Facebook) duba yadda ta hada kowane irin mutane, talaka da mai kudi, kana zaune gida zaka rubuta sako ka saki, kuma Alhamdulillah zaka ga sakon yana isa. Gaskiya tanada anfani sosai a ganina.
Da gaske Marubuci shi ne makaranci?ya kike ganin wannan maganar.
Marubuci dole ya zama makaranci, saboda abinda kake da ‘interest’ akai zaka rubuta, to akwai marubuta da suka yi magana akansa da yawa, karance-karance yana kara buda kwalwar marubuci ne, da rubutu da karatu kamar Hassan da Hussain ne, tare suke tafiya, idan ka rike daya kabar daya lallai za a gane maka ne.
Wane abin farin ciki ne ba za ki taba mantawa da shi ba a rayuwarki?.
Abubuwan farin ciki a rayuwata suna da yawa gaskiya, idan na dauki daya na fada kamar ban yi wa sauran adalci ba ne, amma suna da yawa sosai. Dangane da abubuwan bakin ciki kuma Alhamdulillah gaskiya saidai mu kara gode wa Allah don sune mafi karanci a cikin rayuwata.
Wadanne matsalolin kike fuskanta a dalilin rubutu?
Alhamdulillah da yake dai yanzu nake tasowa, amma tabbas a yanzun ma ina cin moriyar dan motsin da na yi. Matsaloli kuma dama ita rayuwar duka abokiyar tafiyar matsalane, to sai dai mu gode wa Allah.
Wadanne nasarori kika samu a dalilin rubutu?
Alhamdulillah kasancewa ta daya daga wadanda kuka zabi ku yi hira da ita ma ai nasara ne, kuma Alhamdulillah akwai nasarori da na samu da dan dama, tunda akwai da yawan mutane dake tambayata shawara game da matsalolinsu kuma idan na basu shawara a kan dace, to ina jin dadin wannan kuma shima nasara ne a gareni. Ga tarin addu’o’i da kwarin gwiwa da mutane suke bani ina jin dadi sosai.
Ki bayyana mana boyayyiyar baiwarki.
To masha Allah bayan rubutu da na keyi, ni mazanarciya ce wato ‘Artist’, kuma mawakiya ce ni a lokaci guda.
Mun gode sosai.
Ni ma na gode.