Burkina Faso da Mali ba su tura wakilai zuwa taron soja na nahiyar Afirka da Nijeriya ta shirya a ranar litinin ba, yayin da alakar kasashen Sahel da ke karkashin mulkin soja da kuma makwabtansu na yammacin Afirka ke ci gaba da tsami.
Nijar Mali da Burkina Faso da ke karkashin mulkin soja, sun fice daga kungiyar ECOWAS a watan Janairu, bayan da suka kafa nasu kawancen kasashen Sahel (AES) yayin da suka dade suna fafatawa da mayakan jihadi da suka addabi yankin na Sahel.
Nijar, wacce mai kula da tsaron ofishin jakadancin kasar, Kanar Soumana Kalkoye ya wakilta, ita ce kasa daya tilo ta AES a taron shugabannin hafsoshin tsaron Afirka, da aka shirya a Abuja, babban birnin Nijeriya.