Wakilan Nijeriya a gasar cin kofin zakarun nahiyar Afirka ta 2023/2024, Enyimba International Fc dake Aba da Remo Stars FC na Ikenne sun fice daga gasar.
Hakan ya biyo bayan rashin tabuka abin azo a gani a wasan da kungiyoyin biyu suka yi a gida a matakin farko na wasan da suka fafata a Aba da Ikenne.
- CMG Da Hukumar Kwallon Kafar Afirka Ta Kudu Sun Kulla Yarjejeniyar Hadin Gwiwa Da Yin Musaya
- Kwallon Mata: Ingila Ta Kai Wasan Karshe Bayan Doke Australia
Enyimba ta yi kunnen doki ne 0-0 da Al Ahly Benghazi ta Libya a Aba.
Yayin da Remo Stars ta sha kashi da ci 3-2 a bugun fanariti a hannun Medeama SC ta Ghana a Ikenne, Ogun.
Remo tayi rashin nasara a bugun daga kai sai mai tsaron gida inda Madeama Sc suka zura kwallaye uku daga cikin kwallayen da suka buga domin tsallakewa zuwa zagayen farko na gasar.
Yayin da Enyimba, zakarun gasar kwallon kafa ta Najeriya (NPFL) suka sha kashi da ci 4-3 a jimilla.
Enyimba wadanda ake yiwa lakabi da Giwaye tare da Remo Stars duka yanzu za su karkata ga shirye-shiryensu na fara sabon kakar NPFL,wanda ake sa ran za a fara wata mai zuwa.