Mai koyar da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Carlo Ancelotti ya za-ma mai koyarwa na farko da ya lashe gasar cin kofin zakarun turai na Champions League guda hudu a tarihin gasar.
Ranar Asabar Real Madrid ta yi nasara a kan Liber-pool da ci 1-0 a karawar da suka yi a Faransa, inda ta lashe Champions League na 14 jumulla kuma dan wasa Binicius Junior ne ya ci kwallon tilo da ya bai wa kungiyar damar lashe kofin Zakarun Turai na bana, bayan da ta ci La Liga na kakar nan kuma na 35 jumulla.
Ancelotti dan kasar Italiya ya zama na farko da ya dauki Champions League hudu a matakin koci, bayan Bob Paisley da kuma Zinedine Zidane, wadanda kowanne ya lashe sau uku-uku a tarihi.
Haka kuma dan kasar Italiya shi ne kan gaba da ya je wasan karshe karo biyar, ya dauki biyu a Real Madrid da biyu a AC Milan tun bayan da ya fara koyar da Real Ma-drid a shekarar 2014 a Lisbon a kakar farko da ya fara jan ragama, inda Real ta doke Atletico Madrid 4-1.
Karon farko da ya fara daga kofin shi ne a AC Milan a 2003 a filin wasa na Old Traf-ford, inda suka yi nasara a kan Jubentus a bugun daga-kai-sai-mai-tsaron-gida, san-nan ya dauki na biyu a 2007, bayan doke Liberpool 2-1 a Athens.
A Real Madrid kuwa ya lashe Champions League a 2012 da kuma 2022, sannan An-celotti ya shiga jerin masu koyar da Real Madrid da suka dauki Champions League fiye da daya a kungiyar da suka hada da Zidane mai uku da Billalonga mai biyu da kuma Carniglia.
Sauran sun hada da Miguel Muñoz da Del Boskue da kuma Heynckes, wanda ya dauki kofi na bakwai.