Babban bankin Nijeriya (CBN) ya bude kofar shigar da tsohon kudi ta hanyar cike fom duk da an dage shari’ar da ake gabatarwa a kotun koli kan halaccin wa’adin canjin zuwa 22 ga Fabrairu sabanin ranar 10 ga Fabrairu, 2023.
Kotun kolin ta dage ci gaba da shari’ar har zuwa ranar 22 ga watan Fabrairun 2023, ta kuma ce tsohon kudin Naira ya ci gaba da zama halastacce a kan bin doka har sai ta zauna a mako mai zuwa ranar Laraba.
- Tsoffin Kudi: Kotun Koli Ta Dage Sauraren Shari’ar Zuwa 22 Ga Fabrairu
- Kin Bin Umarnin Kotu Kan Batun Canjin Kudi Zai Iya Kawo Koma Baya – Masana
A halin da ake ciki kuma, an bude hanyar ajiye tsofaffin takardun kudi a shafin intanet na babban bankin kasar.
Shafin wanda ke kan cbn.gov.ng, ana buƙatar masu ajiya su cika lambar tabbatar da bayanan su ta (BVN) da lambar waya da adireshin imel da bayanan banki da adadin kudaden da za a ajiye da kuma. bayan haka kuma CBN din ya samar da sashe tuntuba don sanin matsayin mai ajiyar.
A ranar Laraba ne aka fara tsarin ajiye tsofaffin takardun kudin a banki na N200, N500 da N1,000 kuma ana sa ran zai aiki har zuwa ranar Juma’a 17 ga watan Fabrairu.
Don ajiye tsofaffin takardunsu a rassan CBN, za a buƙaci abokan hulda su sami cike fom ɗinsu a yanar gizo, kwafin tantancewa da kuma shaidar shigar da kudi. Da zarar an tabbatar da asusun, za a saka kwatankwacin kuɗin a asusun banki na abokin ciniki.
“Reshen CBN ba sa bude asusu ga daidaikun mutane. Don haka, daidaikun waɗanda suke son saka tsofaffin bayanansu, waɗanda aka sake tsarawa dole ne su sami asusu mai aiki tare da da za su shigar da kudin.