Babban Bankin Nijeriya (CBN), ya fitar da sabbin ka’idojin da suka bai wa masu hada-hadar musayar kudade, damar sayen dalar Amurka har a zuwa adadin 25,000.
CBN, ya sahale masu sayen dalar a duk mako daga gun dilolin Bankuna na musayar kudade, da aka Bankin ya amince da su wato ADB.
- Badakala: Bankin Duniya Ya Kakaba Wa Kamfanoni 2 A Nijeriya Takunkumi
- Babban Bankin Sin: RMB Ya Zama Kudi Na Hudu Mafi Karbuwa Wajen Biya A Duniya
Bankin ya dauki wannan matakin ne, domin a cike bukatar da ake da ita ta kudaden dalar, a kasuwar hada-hadar musayar kudaden.
Wannan sahalewar ta CBN, na kunshe ne, a cikin wata takarda da Mukaddashin riko a sashen kusuwanci da musayar kudade na CBN, Dakta W. J. Kanya ya fitar a madadin CBN.
Kazalika, CBN ya kuma jayyano ka’idojin da ya gindaya, na sayen kudaden, musamam domin a tabbbar da, yin gaskiya da kuma magance sayen kudaden, ba bisa ka’ida ba.
Bugu da kari, Bankin ya jaddada cewa, ya tani hukunci ga duk masu hada-hadar musayar kudaden da suka karya wadannan ka’idoji.
CBN ya ci gaba da cewa, dole ne dilolin su sayar da kudaden musayar ga masu hada-hadar sayar da kudaden, daidai da farashin kasuwar musayar kudade ta kasa, wato NFEM, musamman don a tabbatar da ci gaban tafiyar da farashin.
Bankin ya kuma sanya kashi daya a cikin dari a tsakanin farashin da masu musayar kudaden, za su iya chazar masu sayen kudaden.
“Dole ne dilolin da su gabatar da rahotannin su ga sashen kusuwanci da musayar kudade na CBN, na kudaden da suka sayar ga masu hada-hadar musayar kudaden, inda su kuma masu hada-hadar musayar kudaden, dole ne su rinka gabatar da ribar da suka samu a kullum ta saye da sayar kudaden, ta hanyar amfani da tsarin cibiyoyin hada-hadar kudade, wato FIFd.” In ji CBN.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp