Yau Talata, a yayin taron manema labarai da hukumar inganta cinikayyar kasa da kasa ta kasar Sin wato CCPIT ta saba shiryawa, mai magana da yawun hukumar Sun Xiao ya bayyana cewa, a cikin watanni 3 na karshe a bana, kasar Sin na kara fuskantar matsin lamba a fannin cinikayyar waje. Duk da yanayin mai sarkakiya da ake kara fuskanta a waje, kana abubuwa na rashin tabbas da rashin kwanciyar hankali suna karuwa, amma cinikin wajen kasar Sin yana samun ci gaba yadda ya kamata.
Sun Xiao ya kara da cewa, za a mai da hankali sosai kan sabbin yanayin tattalin arzikin duniya da kuma sabbin bukatun kamfanonin da ke yin cinikin waje, da yin amfani da dandalin zamani, don taimaka musu samun abokan ciniki na kasashen waje.(Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp