ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, July 16, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ce-ce kuce Kan Batun Dakatar Da Sayar Da Barasar Leda

by Leadership Hausa
7 months ago

A kwanan baya ne, ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya ya sanar da dakatar da yin amfani da daukacin sayar da daukacin Barasar da ake sayarwa ta cikin Leda da kuma sauran kayan Lemon Kwalba masu illa da nauyinsu ya wuce ita 200.

Ofishin ya dauki wannan matakin ne, har sai an kammala bincike, kafin ya bayar da umarni na karshe, kan dakatarwar.

  • Sheikh Al-Sudais Ya Gargadi Masu Ibadah Kan Kiyaye Darajar Masallatan Harami
  • ‘Yansanda Sun Kama Mutane 5 Da Ake Zargin ‘Yan Bindiga Ne A Kano.

A cewar ofishin, ya yi nazari a tsanake kan abubuwa da dama da suka hada da irin ilolin da za su iya shafar lafiyar masu amfani da wadannan kayan da shafar tattalin arzikin masu amfani da su.

ADVERTISEMENT

Wannan umarnin na ofishin na dakatar da yin amfani da wadanan kayan na zuwa ne dai, bayan wata muhawa da aka yi, a Majalisar Dattawa da Ma’aikatar Kiwon Lafiya ta Tarayya da kuma Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta kasa wato NAFDAC.

Hukumar ta NAFDAC, ta yi zargin cewa, yawan sarrafa wadannan kayan da kuma yadda masu sayensu ke samun su a cikin sauki domin sayensu, hakan zai iya bayar da dama, ga yara kanana a kasar damar fara shiga harkar yin tu’ammali, da kayan maye tare da kuma bai wasu direbobin motocin haya, damar sayen kayan a cikin sauki, domin kwankwadar kayan a yayin da za su yi tukin motocin.

LABARAI MASU NASABA

M.A. Abubakar Ya Zaɓi Farouk Mustapha A Matsayin Mataimakinsa

Saliba Zai Yi Jinyar Watanni 5 Bayan Raunin Da Ya Samu A Bayansa

Kazalika, an kuma danganta karin samun yawan tashin hankali, a gidajen wasu ma’aurata a kasar nan da kuma aikata manyan ayyukan masha’a a tsakanin wasu ‘yan kasar nan, saboda yin amfani da irin wadannan kayan.

Bisa wani waiwaye da wannan Jaridar ta yi, a watan Disambar 2018 Hukumar NAFDAC da Ma’aikatar Kiwon Lafiya ta Tarayya da kuma Hukumar kula da harkokin masu saye da siyarwa ta Kasa wato FCCPC, suka rabbata hannun yarjejeniya da Kungiyar da Masu Sarrafa Lemon Kwalba ta ta Taba Sigari AFBTE da kuma Kungiyar DIBAN, domin dakatar da sayar da na’ukan Barsar da ake sayarwa a Leda da kuma a cikin kananna Kwalbe.

A cikin waccan yajejeniyar, an sanya dakatarwar za ta fara aiki ne daga ranar 31 ga watan Janiarun 2024, daga baya a kara matsar da wa’adin, zuwa watan Disambar 2025, domin a tabbatar da masana’antun da ke sarrafa wadannan kayan, sun sayar da daukacin kayan da suka sarrafa.

Tun da farko, Darakta Jannar ta NAFDAC Farfesa Mojisola Christianah Adeyeye, da take jaddada wannan matakin na Majalisar Dattawa, ya yi daidai da yarjeniyar Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya na rage yin amfani da Baraza nan da shekarar 2010, wadda ita kanta Nijeriya, ta rabatta hannu a wannan yarjejeniyar.

A cewarta, haramta yin amfani da wadannan kayan an yin i bsa nufin kare lafiyar ‘yan kasar, musamman yara da matasa, domin ba za mu ci gaba da rungume hannu, domin kai samun wata ‘yar riba, ta gajeren lokaci, a jefa lafiyar ‘yan kasar a cikin wata matsala ba.

NAFDAC ta jaddada cewa, kaya biyu ne kawai na Lemon Kwalba da na Leda, aka amince a sarrafa a sayar a kasar wadanda nauyinsu, bai wuce kasa da lita 200 ba.

Sai dai, wannan dkatar sayar da kayan, ya haifar da ce-ce kuce a tsakanin wasu ‘yan kasar, musamman duba da cewa, an dauki matakin ne, bisa nufin durkusar da tattalin arzkin, masu yin sana’ar.

Kazalika, bisa wani bincike a bangaren kiwon lafiya da aka gudanar a kasar nan a A 2024, ya nuna cewa, kauwar shan Barsa ya karu a kasar wanda ya kai ga, an sayar da litar Barasa sama da biliyan 19 da aka sayar a 2025.

Bugu da kari, wata kididdiga ta nuna cewa, yawan matasa da kimanin daga kaso 62 masu shekaru daga 18 zuwa 29, musamman a yankin Arewacin kasar masu amfani da Barasa, sun karu.

Wani bincike ya kuma nuna cewa, an kara samun yawan Ledar da ke dauke da Barasa da ake sayarwa a cikin sauki, wanda hakan ya kara yawan matasa, masu amfani da ita a kasar.

A nan mun lura da cewa, nau’ukan na Ledojin Barasar da suka kai daga Lita 30, 35, ko kuma Lita 50, wasu matasan na samun saukin sayensu.

A gafe daya kuma, akwai batun sauran kayan maye kamar su, Tabawar Wiwi da Koken da Barasa da sauransu da matasa akasari, suke amfani da su, inda irin wadannan kayan, ke haifar da tabin hankali, a tsakaninsu.

Kungiyar masana’antu ta kasa MAN na daya daga cikin wadanda suka nuna adawa, da wannan matakin na dakatar da sarrafa kayan wanda ta yi ikirarin cewa, hakan zai sanya masana’antun cikin gida sama da 500,000 da ke sarrafa wadannan kayan, su tabka asarar da ta kai ta sama da Naira tiriliyan 1.9 na jarin da suka zuba da kuma janyo rashin ayyukan yi.

A cewar kungiyar, dakatarwar za ta bayar da dama ga sauran kamfanonin ketare, damar yin fasakwarin shigo da irin wadannan kayan zuwa cikin kasar nan.

Amma mu a shawarar mu, kamata ya yi, a yi hadaka da hukumomi masu sanya ido kan kayan da ake sarrafawa a kasar da kuma masana’antun kasar, da ke sarrafa kaya a cikin kasar.

Mun kuma yi ammanar cewa, shan Barasa na shafara lafiyar masu amfani da ita, haka kuma masu yin amfani da ita, za su iya kirkiro da wata haramtacciyar hanya domin samun Barasar, wanda hakan zai kara haifar da aikata manyan laifuka.

Wani karin bakin cikin shi ne, yadda wasu jami’an hukumomin da ke da alhahakkin hana yin amfani da kayan mayen, ake samun su dumu-dumu, da cin hanci da rashawa, inda hakan zai iya janyo koma baya, ga kokarin dakatarwar da aka yin na amfani da wadannan kayan.

Ya zama a wajibi a daukai matakan da suka dace, kan ilolin yin amfani da wadannan kayan musamman ta hanyar ilimantarwa da kume killace masu amfani da wadannan kayan, domin a gyara rayuwarsu.

Leadership Hausa
Website |  + postsBio
  • Leadership Hausa
    Tallafa Wa Yara Masu Buƙatu Na Musamman Shi Ne Burina
  • Leadership Hausa
    Dole Mata Su Rungumi Sana’o’i Domin Tsira Daga Takaicin Zamani —Ramatu Bello
  • Leadership Hausa
    Batun Dakile Shan Taba Sigari A Tsakanin Yara A Nijeriya
  • Leadership Hausa
    Har Yanzu Akwai Sauran Rina A Kaba Game Da Makomar Yara A Nijeriya

MASU ALAKA

M.A. Abubakar Ya Zaɓi Farouk Mustapha A Matsayin  Mataimakinsa
Manyan Labarai

M.A. Abubakar Ya Zaɓi Farouk Mustapha A Matsayin Mataimakinsa

July 16, 2026
Saliba Zai Yi Jinyar Watanni 5 Bayan Raunin Da Ya Samu A Bayansa
Manyan Labarai

Saliba Zai Yi Jinyar Watanni 5 Bayan Raunin Da Ya Samu A Bayansa

July 16, 2026
Kotu Ta Yanke Wa Wani Hukuncin Ɗaurin Shekara 7 Kan Tallan Wiwi A Kafafen Sada Zumunta
Manyan Labarai

Kotu Ta Yanke Wa Wani Hukuncin Ɗaurin Shekara 7 Kan Tallan Wiwi A Kafafen Sada Zumunta

July 16, 2026
Next Post
Nijeriya Ta Tabbatar Da Kai Harin Amurka Kan Ƴan Ta’adda A Sokoto

Nijeriya Ta Tabbatar Da Kai Harin Amurka Kan Ƴan Ta’adda A Sokoto

LABARAI MASU NASABA

Ra’yin Sin Da Afirka Ya Zo Daya A Fannin Fasahar AI

Ra’yin Sin Da Afirka Ya Zo Daya A Fannin Fasahar AI

July 16, 2026
Duk Da Sauye-Sauyen Tattalin Arziƙi Kashi 79% Na Ƴan Nijeriya Na Cikin Talauci – Bankin Duniya

Duk Da Sauye-Sauyen Tattalin Arziƙi Kashi 79% Na Ƴan Nijeriya Na Cikin Talauci – Bankin Duniya

July 16, 2026
M.A. Abubakar Ya Zaɓi Farouk Mustapha A Matsayin  Mataimakinsa

M.A. Abubakar Ya Zaɓi Farouk Mustapha A Matsayin Mataimakinsa

July 16, 2026
Saliba Zai Yi Jinyar Watanni 5 Bayan Raunin Da Ya Samu A Bayansa

Saliba Zai Yi Jinyar Watanni 5 Bayan Raunin Da Ya Samu A Bayansa

July 16, 2026
Kotu Ta Yanke Wa Wani Hukuncin Ɗaurin Shekara 7 Kan Tallan Wiwi A Kafafen Sada Zumunta

Kotu Ta Yanke Wa Wani Hukuncin Ɗaurin Shekara 7 Kan Tallan Wiwi A Kafafen Sada Zumunta

July 16, 2026
Tinubu Yana Zuba Kyawawan Ayyuka A Nijeriya – Ganduje

Ganduje Ya Buƙaci A Yi Siyasar Aƙida Domin Inganta Dimokuraɗiyya A Nijeriya

July 16, 2026
Binciken CGTN: Amfanar Da Kowa Da Kowa Shi Ne Ainihin Alherin Da Fasahohin Kwaikwayon Tunanin Bil Adama Suka Kawo

Binciken CGTN: Amfanar Da Kowa Da Kowa Shi Ne Ainihin Alherin Da Fasahohin Kwaikwayon Tunanin Bil Adama Suka Kawo

July 15, 2026
Sin Ta Yi Kira Da A Kafa Tsarin Jagorantar Muhimman Ma’adinai Ga Sauyawa Zuwa Amfani Da Makamashi Mai Tsafta

Sin Ta Yi Kira Da A Kafa Tsarin Jagorantar Muhimman Ma’adinai Ga Sauyawa Zuwa Amfani Da Makamashi Mai Tsafta

July 15, 2026
Gwamna Dauda Lawal Zai Gabatar Da Jawabi A Taron Ƙasa Da Ƙasa Na Jami’ar FUE Zariya

Gwamna Dauda Lawal Zai Gabatar Da Jawabi A Taron Ƙasa Da Ƙasa Na Jami’ar FUE Zariya

July 15, 2026
Neman Raba-Gari Da Sauran Kasashe Zai Kawo Mummuann Tasiri Ga Bangarorin Da Abin Ya Shafa

Neman Raba-Gari Da Sauran Kasashe Zai Kawo Mummuann Tasiri Ga Bangarorin Da Abin Ya Shafa

July 15, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.