Wani binciken jin ra’ayin jama’a na duniya da masanan CGTN da cibiyar nazarin jin ra’ayin jama’a ta jami’ar Renmin ta kasar Sin suka kaddamar, ya nuna cewa, wadanda aka ji ra’ayoyinsu a duniya sun ba da muhimmanci kan muhimman hakkokin bil-adama, kamar ‘yancin rayuwa da raya kasa. Kashi 84.8 cikin 100 na wadanda suka bayar da amsa a duniya sun yi imanin cewa, babu wata demokraɗiyya da ta dara wata. Demokradiyya mafi kyau, ita ce wacce ta dace da yanayin kasar. (Ibrahim Yaya)
Talla