An bayyana dan takarar jam’iyyar Labour Party (LP) a zaben gwamnan jihar Abia da aka gudanar ranar Asabar, Alex Otti, a matsayin wanda ya lashe zaben jihar.
Otti, wanda fitaccen ma’aikacin banki ne, ya samu kuri’u mafi rinjaye 175,467. Dan takarar jam’iyyar PDP mai mulki Okey Ahiwe ne ke mara masa baya da kuri’u 88,529.
PDP ce ke mulkin jihar tun bayan komawar mulkin dimokuradiyya a 1999.
Jami’in da ke kula da zaben kuma mataimakin shugaban jami’ar fasaha ta tarayya ta Owerri, jihar Imo, Farfesa Nnenna Nnannaya Oti ne ya bayyana wanda ya lashe zaben a hukumance bayan kammala tattara sakamakon zaben da aka gudanar a ranar Laraba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp