Tsohon dan wasan tsakiya na Arsenal da Real Madrid da kasarsa Jamus, Mesut Ozil, ya sanar da yin ritaya daga buga kwallon kafa yana da shekaru 34.
Ozil ya lashe kofuna tara a lokacin rayuwarsa a kulob da suka hada da Kofin FA hudu da kofin La Liga na Spain a shekarar 2012.
Ya kuma ci wa Jamus wasanni 92 kuma yana cikin tawagar da ta dauki kofin duniya a Brazil a shekara ta 2014.