Tsohon dan wasan bayan Italiya da Juventus, Giorgio Chiellini ya yi ritaya daga murza tamola.
Dan wasan mai shekaru 39 a duniya ya sanar da ajiye takalamansa ne cikin wani sakon bidiyo da ya saki a kafafen sada zumunta.
- NLC Ta Yi Barazanar Sake Shiga Yajin Aiki
- Jami’in MDD: Kasar Sin Ta Ba Da Babbar Gudummawa Ga Wadatar Abinci A Duniya
Chiellini ya kare wasansa ne a gasar MLS ta kasar Amurka, inda kungiyarsa ta Los Angeles FC ta yi rashin nasara a wasan karshe na kofin MLS Cup a hannun kungiyar Columbus Crew.
Chiellini ya fara yi wa Juventus wasa a 2005, wanda daga nan ya zamo jigon dan wasa a kungiyar.
Dan wasan ya lashe gasar Serie A tara a jere da Juventus, amma bai taba lashe gasar zakarun turai ba amma dai ya je wasan karshe har sau biyu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp