China ta mayar da martani ga barazanar Shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, na ƙara harajin kashi 10% akan ƙasashen da ke goyon bayan ƙungiyar BRICS, inda ta bayyana cewa BRICS ba ƙungiyar adawa bace kuma bata nufin wata ƙasa da mugunta.
Trump ya bayyana a dandalin Truth Social cewa duk ƙasar da ta nuna goyon baya ga manufofin BRICS ko “tsarin adawa da Amurka,” za a ƙaƙabawa ƙarin haraji ba tare da rangwame ba.
- Trump Ya Yi Barazanar Ƙarin Haraji Ga Ƙasashen Da Suka Rungumi BRICS
- Isra’ila Ta Amince Da Tsagaita Wuta Na Tsawon Kwana 60 Da Hamas – Trump
Mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen China, Mao Ning, ta bayyana a wata ganawa da manema labarai cewa BRICS wata kafa ce ta haɗin gwuiwa tsakanin ƙasashe masu tasowa da ke neman ci gaba.
Ta bayyana BRICS a matsayin ƙungiya mai buɗaɗɗen hali da haɗin kai, ba mai tayar da husuma ba. Ta kara da cewa “Yaƙin tattalin arziki da ƙara haraji ba su da riba, kuma ƙare-ƙaren farashin kasuwa ba zai kai ga ci gaba ba.”
Trump ya kuma bayyana cewa zai fara tura wasiƙun haraji ko sanar da sabbin yarjejeniyoyin kasuwanci daga ranar 7 ga watan Yuli, yayin da hutu na kwana 90 da ya ɗauka kan sabbin haraji ke dab da ƙarewa. Ya ce harajin da ya shirya na da matukar muhimmanci wajen tilasta sabbin yarjejeniyoyin ciniki da farfaɗo da masana’antu a Amurka, musamman domin rage rinjayen China a wasu muhimman fannoni.
A taron ƙungiyar BRICS na karo na 17 da aka gudanar a Brazil, ƙasashen mambobi da suka haɗa da China, India, Rasha, Saudi Arabia, Iran da wasu sun soki hauhawar haraji da manufofin kariya ta ciniki da wasu ƙasashe ke aiwatarwa. A sanarwar da suka fitar, sun nuna damuwa kan rikicin Gabas ta Tsakiya, amma sun kaucewa sukar Rasha kai tsaye dangane da rikicin Ukraine.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp