Shugaban China, Xi Jinping ya yi alkawarin dorawa kan alakar tattalin arziki da Nijeriya, inda ya ce kasar na da muhimmanci ga Afirka da kuma duniya baki daya.
Shugaban na China ya yi magana ne ta bakin jakadansa na musamman, Peng Qinghua, wanda ya gana da sabon shugaban Nijeriya, Bola Ahmad Tinubu a fadarsa da ke Abuja.
- Za Mu Dauki Kwakkwaran Mataki Idan Gwamnati Ta Janye Tallafin Man Fetur —NLC
- Akwai Wadataccen Mai Da Zai Ishi ‘Yan Kasa Nan Da Kwanaki 30 —NNPCL
Qinghua ya ce kasashen biyu suna da kyakkyawar dangantaka ta fuskar kasuwanci da tattalin arziki yana mai cewa kamfanonin China na tafiyar da harkokinsu da kyau a bangaren hanyoyi da layin dogo.
Tinubu ya tabbatar da ganawar tasu a wani sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter, inda ya ce “na karbi bakuncin jakada na musamman na shugaban China, Xi Jinping. Ina fatan ganin alakar diflomasiyya mai karfi da karuwar huldar kasuwanci tsakanin kasashenmu biyu.”