ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, November 14, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ci Gaban Kasar Sin Dama Ce Ba Kalubale Ba

by CMG Hausa
2 years ago
Kasar Sin

Kalaman shugaban kasar Sin Xi Jinping, yayin da yake zantawa da sakataren harkokin wajen Amurka dake ziyara a kasar Sin Anthony Blinke, sun bayyana wasu muhimman batutuwan jan hankali ga Amurka.

Zan iya cewa kalaman wata manuniya ce ga Amurka cewa, hanyar da ta dauka ba za ta bulle ba, kana jan hankali ne gare ta ta gyara kura-kuranta.

  • Aiwatar Da Alkawain Da Aka Yi Yana Da Muhimmanci

A cewar Shugaba Xi, takarar manyan kasashen duniya ba ta wakiltar yanayin da ake ciki, hakan kuma ba zai taba iya magance matsalolin Amurka ko kalubalen da duniya ke fuskanta ba. Tabbas bai kamata yayin da ake fuskantar kalubale masu tsanani a duniya, babbar kasa kamar Amurka ta rika mayar da hankali kan takara ko yada jita-jita ba. Babu abun da wadannan abubuwa za su haifar face kara tada hankalin duniya da ta’azzara matsalolin da ake fuskanta.

ADVERTISEMENT

Amurka ta kasance mai yin amai, kuma ta lashe. Ta kan nace cewa ba ta neman takara da kasar Sin ko kuma ba ta goyon bayan ’yancin yankin Taiwan na kasar, sai dai ayyukanta na yin hannun riga da abubuwan da take furtawa. A halin da ake ciki, duniya na bukatar Amurka mai sanin ya kamata da cika alkawarin da ta dauka da dakatar da kirkiro matsaloli ko ma kokarin karkatar da hankalin duniya daga yanayin da ake ciki.

A kalaman shugaba Xi, ya kamata kasashen su girmama muradun kowannensu, haka kuma, nasarorin da za su samu, dama ce maimakon barazana. Har kullum burin kasar Sin shi ne ganin ci gaban kasashe, yayin da Amurka ke daukar hakan a matsayin barazana.

LABARAI MASU NASABA

Kalubalantar Ka’idar “Kasar Sin Daya Tak A Duniya” Tamkar Wasa Da Wuta Ne

Sin: Ya Zama Wajibi Japan Ta Janye Kalamanta Dangane Da Taiwan 

Doka ta ba kowacce kasa damar samun ci gaba, don haka, bai kamata wata kasa taya tilo ta kasance mai babakere ko bayar da izinin samun ci gaba ga sauran kasashe ba. Misali, kasar Sin ta samu ci gaba ne bisa jajircewarta, da hikimomi da basirar al’ummarta da ma tsarin shugabanci na kwarai, don haka babu wata kasa dake da izini ko damar iyakancewa ko kayyade ci gabanta. Ya dace Amurka da kawayenta su sakar ma Sin da ma sauran kasashe mara, su raya kansu ta yadda suke ganin ya fi dacewa da yanayinsu. Wannan a ganina, shi zai kai duniya ga samun ci gaba har ma da zaman lafiya. Kai ya riga ya waye, manufofin kasar Sin sun bambanta da na kasashen yamma, karfin kasar Sin ba ya nufin za ta yi wa duniya babakere. Har ila yau, ci gaban kasar Sin na zama dama ne ga kasashe masu burin raya kansu, Amurka da kanta na iya amfana daga hakan idan ta sauke girman kai da neman babakere.

Duk da kalubalen dake akwai da ma dimbin banbance-bambance, a matsayinsu na manyan kasashe dake zama abun koyi ga kasashe masu tasowa, har yanzu lokaci bai kurewa Sin da Amurka ba na lalubo hanyoyin inganta dangankarsu ko da kuwa za su yi hakan ne a hankali.

Duniya na bukatar hadin kansu, duba da kasancewarsu manya, dama tasirin da Sin ke da shi tsakanin kasashe masu tasowa mafi rinjaye, don haka ya dace su yi la’akari da hakan don tabbatar da zaman lafiya da dunkulewar da ake muradi a duniya. (Faeza Mustapha)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Kalubalantar Ka’idar “Kasar Sin Daya Tak A Duniya” Tamkar Wasa Da Wuta Ne
Daga Birnin Sin

Kalubalantar Ka’idar “Kasar Sin Daya Tak A Duniya” Tamkar Wasa Da Wuta Ne

November 14, 2025
Sin: Ya Zama Wajibi Japan Ta Janye Kalamanta Dangane Da Taiwan 
Daga Birnin Sin

Sin: Ya Zama Wajibi Japan Ta Janye Kalamanta Dangane Da Taiwan 

November 13, 2025
Li Qiang Zai Halarci Tarukan SCO Da G20 Tare Da Ziyarar Aiki A Zambia
Daga Birnin Sin

Li Qiang Zai Halarci Tarukan SCO Da G20 Tare Da Ziyarar Aiki A Zambia

November 13, 2025
Next Post
Gwamnatin Kano Ta Fara Bincike Kan Zaftare Wa Ma’aikata Albashi

Gwamnatin Kano Ta Fara Bincike Kan Zaftare Wa Ma'aikata Albashi

LABARAI MASU NASABA

GORON JUMA’A

GORON JUMA’A

November 14, 2025
Kalubalantar Ka’idar “Kasar Sin Daya Tak A Duniya” Tamkar Wasa Da Wuta Ne

Kalubalantar Ka’idar “Kasar Sin Daya Tak A Duniya” Tamkar Wasa Da Wuta Ne

November 14, 2025
Musulmin da Aka Kashe  A Zamfara, Katsina Da Sokoto Sun Ninka Na Kiristoci A Tsakiyar Najeriya: MACBAN

Musulmin da Aka Kashe  A Zamfara, Katsina Da Sokoto Sun Ninka Na Kiristoci A Tsakiyar Najeriya: MACBAN

November 14, 2025
Manzon Allah (SAW) A Matsayin Dan Gatan Allah 

Manzon Allah (SAW) A Matsayin Dan Gatan Allah 

November 14, 2025
Fansho Da Garatuti A Kano: Yau Fari Gobe Tsumma: Martani

Fansho Da Garatuti A Kano: Yau Fari Gobe Tsumma: Martani

November 14, 2025
Kofin Duniya: Nijeriya Za Ta Fafata Da DR Congo A Wasan Ƙarshe

Kofin Duniya: Nijeriya Za Ta Fafata Da DR Congo A Wasan Ƙarshe

November 14, 2025
Masana’antu Masu Zaman Kansu A Arewa Sun Yi Maraba Da Harajin Kashi 15 Na Shigo Da Man Fetur

Masana’antu Masu Zaman Kansu A Arewa Sun Yi Maraba Da Harajin Kashi 15 Na Shigo Da Man Fetur

November 14, 2025
Ronaldo Na Fuskantar Dakatarwar Wasanni Biyu Bayan Samun Jan Kati

Ronaldo Na Fuskantar Dakatarwar Wasanni Biyu Bayan Samun Jan Kati

November 14, 2025
Editoci Sun Yi Gargadi Kan Rushewar Kafofin Yada Labarai Sakamakon Matsin Tattalin Arziki

Editoci Sun Yi Gargadi Kan Rushewar Kafofin Yada Labarai Sakamakon Matsin Tattalin Arziki

November 14, 2025
Kotu Ta Yanke Wa Mutum 4 Hukuncin Kisa Kan Kashe Wani Makanike A Kano

Kotu Ta Yanke Wa Mutum 4 Hukuncin Kisa Kan Kashe Wani Makanike A Kano

November 14, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.