Cibiyar binciken sararin samaniya ta kasar Sin DSEL na gayyatar baki masu basira da su nemi gurbi a shirinta mai taken “2023 Overseas Outstanding Young Talents Program” na matasa masu basira daga kasashen waje, domin inganta aikin binciken sararin samaniya.
A cewar DSEL, shirin, wanda gidauniyar raya harkokin kimiyya ta kasar Sin ta samar da kudin aiwatar da shi, na da nufin jan hankalin matasa masu basira daga kasashen waje, wadanda suka cimma nasarori a bangaren kimiyya da injiniya da fasaha, don su zo kasar Sin su yi aiki.
Ana gayyatar masu neman shiga shirin da su shiga cikin binciken kimiyya da fasahar sufurin sararin samaniya da kimiyyar sararin samaniya da na duniyoyi daban daban da bangaren Physics da ilimin taurari da kimiyya da fasahar makamashin nukiliya da nazarin halittu da Chemistry da fasahar sadarwa da AI da sauransu.
Manufar cibiyar ita ce, inganta dorewar ayyukan binciken sararin samaniya da suka shafi wata da duniyoyi da kuma rana. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp