• English
  • Business News
Monday, October 27, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Cibiyar Kimiyyar Noma Na Sin CATAS Ta Cancanci Yabo

by CGTN Hausa
2 years ago
CATAS

Kasar Congo Brazzaville wadda ke yankin tsakiyar Afirka, na da albarkatun noma baya ga danyen mai, kuma ’yan kasar na alfahari, da cin gajiya daga sana’ar noma, to amma aikin noma a wannan zamani na bukatar kwarewa, sanin makamar aiki, da amfani da fasahohin zamani domin samun cikakkiyar gajiya.

Bisa hakan ne ma cibiyar kimiya ta bunkasa noma a yankuna masu zafi ta kasar Sin ko CATAS, ta kuduri aniyar horas da manoma da jami’ai a Congo, dabarun amfani da na’urorin zamani na inganta wannan sana’a. A baya bayan nan, jami’an wannan cibiya ta CATAS sun gudanar da irin wannan horo a birnin Haikou, fadar mulkin lardin Hainan na kasar Sin. Kazalika wasu jami’an cibiyar ta CATAS sun gabatarwa daliban Congo dabarun kimiyya na bunkasa noma a wasu gonakin dake kusa da birnin Brazzaville, fadar mulkin kasar ta Congo.

  • Kasar Sin Mai Burin Ganin Ci Gaban Kowa
  • Sin Ta Harba Sabon Tauraron Dan Adam Na Hangen Nesa

A cikin shekaru biyar, kwararru daga CATAS dake aiki a Brazzaville, suka gudanar da horaswa har sau 29, inda suka gabatarwa manoman kasar, da jami’an sashen noma dabaru daban daban na wanzar da ci gaban sana’ar noma a kasar.

Ko shakka babu, kwararru a wannan muhimmin fanni na noma daga kasar Sin, sun shuka wata muhimmiyar alaka ta inganta noma, musamman a yankunan wannan kasa mai dumi dake tsakiyar Afirka, wanda hakan ya sanya dan ba ga inganta hadin gwiwar Sin da nahiyar Afirka.

Karkashin kwazon wadannan kwararru na cibiyar CATAS, an tura sama da rukunin masana 20 zuwa Congo, domin su gudanar da tallafin horaswa na inganta fasahar noma, suna kuma ci gaba da aiki a cibiyar gwaji ta “ATDC” tun daga shekarar 2007 kawo yanzu.

LABARAI MASU NASABA

Tunawa Da Dawowar Taiwan Kasar Sin Shekaru 80 Da Suka Wuce Yana Da Ma’ana Sosai

Kara Bude Kofofin Sin Zai Samar Da Karin Gajiya A Fannin Bunkasar Duniya

Ana iya ganin tasirin wannan muhimmin aiki a Congo, inda manoman wurin ke gwada sabbin iri na yanayin zafi, da noman kaji, da sauran sassan bunkasa noma.

Tabbas, a sana’ar noma, samun kwarewa, ta amfani da kimiyya da fasahohin zamani, jigo ne na cimma nasarar da ake fata. A wannan gaba da Congo Brazzaville ke more fasahohin kwararru daga kasar Sin, muna iya cewa hakan abun a yaba ne, kuma yana kara nuna aniyar kasar Sin ta yada fasahohinta na ci gaba, ga sauran kasashe masu tasowa dake nahiyar Afirka.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Tunawa Da Dawowar Taiwan Kasar Sin Shekaru 80 Da Suka Wuce Yana Da Ma’ana Sosai
Daga Birnin Sin

Tunawa Da Dawowar Taiwan Kasar Sin Shekaru 80 Da Suka Wuce Yana Da Ma’ana Sosai

October 26, 2025
Kara Bude Kofofin Sin Zai Samar Da Karin Gajiya A Fannin Bunkasar Duniya
Daga Birnin Sin

Kara Bude Kofofin Sin Zai Samar Da Karin Gajiya A Fannin Bunkasar Duniya

October 26, 2025
Ya Zuwa Satumban Bana Adadin Lantarki Da Sin Ta Samar Ya Karu Da Kaso 17.5%
Daga Birnin Sin

Ya Zuwa Satumban Bana Adadin Lantarki Da Sin Ta Samar Ya Karu Da Kaso 17.5%

October 26, 2025
Next Post
Adadin Jarin Da Kasar Sin Ta Zuba A Kasashen Waje A Shekarar 2022 Na Kan Gaba A Duniya

Adadin Jarin Da Kasar Sin Ta Zuba A Kasashen Waje A Shekarar 2022 Na Kan Gaba A Duniya

LABARAI MASU NASABA

An Zaɓi Birgediya Janar Yake A Matsayin Sarkin Sayawa Na Farko Duk Da Zanga-zanga 

An Zaɓi Birgediya Janar Yake A Matsayin Sarkin Sayawa Na Farko Duk Da Zanga-zanga 

October 27, 2025
CATAS

Tsohon Gwamnan Jigawa, Lamido Ya Bayyana Aniyar Takarar Shugabancin Jam’iyyar PDP Na Ƙasa

October 27, 2025
Sojoji Sun Kashe ‘Yan ta’adda 10, Sun Ƙwato Makamai A Borno

Sojoji Sun Kashe ‘Yan ta’adda 10, Sun Ƙwato Makamai A Borno

October 27, 2025
Hatsarin Jiragen Ruwa

Matasa 5 Sun Mutu A Hatsarin Jirgin Ruwa A Gombe

October 27, 2025
Tunawa Da Dawowar Taiwan Kasar Sin Shekaru 80 Da Suka Wuce Yana Da Ma’ana Sosai

Tunawa Da Dawowar Taiwan Kasar Sin Shekaru 80 Da Suka Wuce Yana Da Ma’ana Sosai

October 26, 2025
Matatar Dangote Za Ta Faɗaɗa Ƙarfin Aiki Zuwa Ganga Miliyan 1.4 Kullum

Matatar Dangote Za Ta Faɗaɗa Ƙarfin Aiki Zuwa Ganga Miliyan 1.4 Kullum

October 26, 2025
Kara Bude Kofofin Sin Zai Samar Da Karin Gajiya A Fannin Bunkasar Duniya

Kara Bude Kofofin Sin Zai Samar Da Karin Gajiya A Fannin Bunkasar Duniya

October 26, 2025
“Ba Gudu Ba Ja Da Baya Game Da Tsarin “Call-up system” A NPA”

“Ba Gudu Ba Ja Da Baya Game Da Tsarin “Call-up system” A NPA”

October 26, 2025
Ya Zuwa Satumban Bana Adadin Lantarki Da Sin Ta Samar Ya Karu Da Kaso 17.5%

Ya Zuwa Satumban Bana Adadin Lantarki Da Sin Ta Samar Ya Karu Da Kaso 17.5%

October 26, 2025
Dalilin Da Suka Sa Hisbah Ta Dakatar Da Auren Ƴan TikTok A Kano

Dalilin Da Suka Sa Hisbah Ta Dakatar Da Auren Ƴan TikTok A Kano

October 26, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.