Cibiyoyin hada-hadar kudi na kasashen waje sun bayyana kwarin gwiwa kan makomar tattalin arzikin kasar Sin, yayin da kasar take samun kyakkyawar sakamakon yunkurin samun bunkasuwa sannu a hankali.
Bayanai na baya-bayan nan da hukumar kididdigar ta kasar Sin (NBS) ta fitar sun nuna cewa, a cikin watannin shida na farkon bana, GDPn kasar ya karu da kashi 5 cikin dari idan aka kwatanta da makamancin lokacin a bara.
- Aboki Mai Natsuwa Shi Ne Wanda Ake Iya Dogaro A Kansa
- Ambaliyar Ruwa Ta Yi Sanadin Mutuwar Mutane 8 A Lardin Sichuan Na Sin
Wu Yibing, shugaban kamfanin hannun jarin Singapore Temasek reshensa dake kasar Sin ya ce, tattalin arzikin Sin ya samu fa’ida ne daga bincike da kirkire-kirkire.
Yawan mutum-mutumi masu ba da hidima, da wayoyin salula da motocin sabbin makamashin da aka samar a kasar ya karu da kashi 22.8 cikin dari da kashi 11.8 da kuma kashi 34.3 cikin dari bi da bi a cikin watanni shidan farkon bana.
Babban kamfanin Bloomberg na kasar Amurka ya bayyana a cikin wani rahoto a ranar 16 ga watan Yuli cewa, kokarin da kasar Sin ke yi na dogon lokaci na samun ci gaba mai inganci ya fara samun kyakkyawar sakamako.
Rahoton ya ce, ci gaban da aka samu a motocin lantarki da farantan makamashin hasken rana da sauran masana’antun fasahar zamani sun taimaka wajen ci gaban bunkasar tattalin arzikin da ya kai kusan kashi 5 cikin dari. (Mai fassara: Yahaya)