ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, November 15, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

CICPE Na 2024 Dama Ce Ga Kasashen Ketare Ta Fahimtar Kasuwar Sin

by CGTN Hausa
2 years ago
CICPE

Baje kolin kayayyakin masarufi na kasa da kasa na kasar Sin karo na 4 ko CICPE a takaice, wanda aka fara daga ran 13 ga wannan watan a Haikou, babban birnin lardin Hainan, shi ne baje kolin kasa da kasa na farko na kasar Sin na kayayyakin masarufi, kuma mafi girma a yankin Asiya da tekun Pasifik.

A matsayin baje kolin kasa da kasa na farko a kasar Sin a shekarar 2024, ya taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa harkokin cinikayya a tsakanin kasar Sin da sauran kasashe da kuma kara habaka shigo da kayayyaki masu inganci. Musamman ma, ya kasance wata kafa ga kamfanoni na kasa da kasa don samun damar shiga babbar kasuwar kayayyakin masarufi na kasar Sin wadda ta kasance daya daga cikin mafi girma da kuma saurin bunkasuwa a duniya, kuma babbar dama ga ‘yan kasuwan duniya wajen tallata hajojinsu.

  • “Karamin Rukuni” Na Amurka Da Japan Da Philippines Ya Kawo Illa Ga Kwanciyar Hankali A Tekun Kudancin Kasar Sin
  • Babu Inda Mayaudara Da Mahassada Suka Taru Kamar Masana’antar Kannywood – Adam Zango

Baje kolin na bana ya zarce wanda aka gudanar a baya da girman fili mai fadin murabba’in mita 128,000, kuma ya hada kayayyakin masarufi masu inganci daga gida da waje, da masu saya da sayarwa daga duk fadin duniya, tare da ba da gudummawa wajen fadada kasuwannin kayayyakin masarufi na kasar Sin, da kuma biyan bukatar kayayyaki na musamman kuma masu inganci.

ADVERTISEMENT

Baje kolin ya bayyana karfin saya da sayarwa na jama’ar kasar Sin, domin ya gabatar da sabbin kayayyaki na zamani da ake bukata, da kayayyaki daban-daban na kasa da kasa ga mahalarta, da wadatar zabi ga masu sayayya bisa bukatunsu, da kuma bunkasa kasuwar kayayyakin masarufi a kasar Sin.

An zabi Ireland a matsayin babban bako na baje kolin kayayyakin masarufi na kasa da kasa na bana wanda ke gudana daga ranar 13 zuwa 18 ga watan Afrilu, yayin da Italiya, Faransa, Jamhuriyar Czech, Japan, Kanada da Switzerland suka kafa rumfunan a matsayin mahalarta na kasa da kasa.

LABARAI MASU NASABA

Bangaren Sauka Na Kumbon Shenzhou-21 Ya Iso Doron Duniya

Sin Za Ta Mayar Da Martani Idan Har Japan Ta Aiwatar Da Matakin Da Bai Dace Ba

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Bangaren Sauka Na Kumbon Shenzhou-21 Ya Iso Doron Duniya
Daga Birnin Sin

Bangaren Sauka Na Kumbon Shenzhou-21 Ya Iso Doron Duniya

November 14, 2025
Sin Za Ta Mayar Da Martani Idan Har Japan Ta Aiwatar Da Matakin Da Bai Dace Ba
Daga Birnin Sin

Sin Za Ta Mayar Da Martani Idan Har Japan Ta Aiwatar Da Matakin Da Bai Dace Ba

November 14, 2025
Jirgin Ruwan Dakon Jiragen Saman Yaki Na Sichuan Ya Fara Gwajin Sufuri A Karon Farko
Daga Birnin Sin

Jirgin Ruwan Dakon Jiragen Saman Yaki Na Sichuan Ya Fara Gwajin Sufuri A Karon Farko

November 14, 2025
Next Post
Gwamnatin Katsina Ta Raba Wa Jami’an Tsaro Sabbin Motocin Yaki

Gwamnatin Katsina Ta Raba Wa Jami'an Tsaro Sabbin Motocin Yaki

LABARAI MASU NASABA

Bangaren Sauka Na Kumbon Shenzhou-21 Ya Iso Doron Duniya

Bangaren Sauka Na Kumbon Shenzhou-21 Ya Iso Doron Duniya

November 14, 2025
NAHCON Ta Ƙaddamar Da Kwamitin Da Zai Kula Da Shafin Nusuk Masar Na Hajjin 2026

NAHCON Ta Ƙaddamar Da Kwamitin Da Zai Kula Da Shafin Nusuk Masar Na Hajjin 2026

November 14, 2025
NSCDC Ta Cafke Mutum Biyu Bisa Zargin Satar NAPEP Da Safarar Miyagun Kwayoyi A Kano

NSCDC Ta Cafke Mutum Biyu Bisa Zargin Satar NAPEP Da Safarar Miyagun Kwayoyi A Kano

November 14, 2025
Gwamnan Gombe Ya Gabatar Da Naira Biliyan 535.69 A Matsayin Kasafin 2026

Gwamnan Gombe Ya Gabatar Da Naira Biliyan 535.69 A Matsayin Kasafin 2026

November 14, 2025
Sin Za Ta Mayar Da Martani Idan Har Japan Ta Aiwatar Da Matakin Da Bai Dace Ba

Sin Za Ta Mayar Da Martani Idan Har Japan Ta Aiwatar Da Matakin Da Bai Dace Ba

November 14, 2025
Tinubu Ya Zuba Naira Tiriliyan 1.5 Don Bunkasa Noma Da Kayan Aiki Na Zamani

Tinubu Ya Zuba Naira Tiriliyan 1.5 Don Bunkasa Noma Da Kayan Aiki Na Zamani

November 14, 2025
Jirgin Ruwan Dakon Jiragen Saman Yaki Na Sichuan Ya Fara Gwajin Sufuri A Karon Farko

Jirgin Ruwan Dakon Jiragen Saman Yaki Na Sichuan Ya Fara Gwajin Sufuri A Karon Farko

November 14, 2025
Rashin Daukar Tsauraran Matakai Na Iya Durkusar Da Bangaren Noma – Shehu Galadima

Dalilin Asusun NADF Na Yin Hadaka Da Gwamnatin Jihar Jigawa

November 14, 2025
Xi Jinping Ya Gana Da Sarkin Thailand

Xi Jinping Ya Gana Da Sarkin Thailand

November 14, 2025
BUK Za Ta Kafa Cibiyar Horas da Aikin Jarida da Sabbin Kafofin Sadarwa Na Zamani

BUK Za Ta Kafa Cibiyar Horas da Aikin Jarida da Sabbin Kafofin Sadarwa Na Zamani

November 14, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.