Baje kolin zuba jari da cinikayyar kasa da kasa na kasar Sin ko CIFIT a takaice, da ake gudanarwa kowace shekara a birnin Xiamen na lardin Fujian dake gabashin kasar Sin, ba sa kaimi ga kasashen waje da su zuba jari a kasar Sin kawai yake yi ba, har ma da saukaka zuba jarin Sin a kasashen waje. Kana, yana mai da hankali kan hadin gwiwar cinikayya tsakanin bangarori daban daban, da habaka hadin gwiwa a fannoni masu mahimmanci kamar sauyi zuwa amfani da fasahohin dijital, da masana’antu mara gurbata muhalli, da sabbin fasashohi masu tasowa.
An fara baje kolin CIFIT na 2024, mai taken “Hada Duniya ta Hanyar Zuba Jari” ne a ranar 8 ga watan Satumba. Wanda ke da nufin karfafa matsayinsa na cibiyar zuba jari ta duniya, kuma jadawalin mahalarta baje kolin ya hada da hukumomin gwamnati, da kungiyoyin masana’antu, da manyan kamfanoni na kasa da kasa, da kungiyoyin kasa da kasa, da masu sha’awar kara fahimtar yanayin zuba jari daga sama da kasashe 90.
- Mataimakin Firaministan Sin Ya Karfafa Gwiwar Kamfanonin Waje Da Su Shiga Aikin Sin Na Neman Samun Bunkasuwa Mai Inganci
- Xi Ya Rattaba Hannu Kan Umarnin Amfani Da Ka’idojin Kare Muhalli A Aikin Soja
Sau da yawa ana yiwa baje kolin lakabi da “barometer” ko “compass” wato ma’auni ko alkibla na zuba jarin waje da na cikin gida na kasar Sin, wanda ya kasance mataki mara misaltuwa na cudanya da habaka tattalin arziki a duniya. To, wane tasiri baje kolin na bana zai yi ga bude kofa ga kasashen waje da ma zuba jari?
Da farko dai CIFIT zai ba da haske game da dabarun kasar Sin wajen samar da hannun jarin Sin a cikin gida da waje. Ta yadda mahalarta baje kolin za su samu karin haske kan sabbin manufofin cinikayyar kasar Sin, da dabarun gudanar da ayyukan ci gaban duniya, da gudummawar da take bayarwa ga hadin gwiwar tattalin arzikin kasa da kasa.
CIFIT zai kuma karfafa ayyukan zuba jari a kasar Sin, da yayata sabon karfin samar da hajoji da hidimomi masu karko tare da masana’antu masu amfani da kirkirarriyar basira (AI), da kimiyyar rayuwa, da fasahar samar da kayayyakin amfani maras gurbata muhalli. Wannan yunkuri, wanda zai ba da damammaki iri-iri, zai karfafa matsayin Sin a sahun gaba na zuba jari a duniya.