A matsayin baje kolin farko a duniya a matakin kasa, wanda ke mayar da hankali ga hada-hadar shigo da hajoji daga kasashen waje zuwa Sin, Baje koli na CIIE, ya zama muhimmin matakin kasar Sin na inganta sabon tsarin ci gaba, kuma dandamali na karfafa manufar bude kofa ga waje.
A yayin baje kolin CIIE na bana, an samu halartar kamfanoni 4,142, daga kasashe da yankuna 148 na ketare, adadin da ya kasance mafi yawa a tarihin wannan taro. Adadin kamfanonin da ke cikin jerin mafiya girma a duniya ko ‘Fortune Global 500’, da manyan kamfanoni masu jagoranci a fannoni daban-daban da ke halartar baje kolin na bana, ya zarce 300 a karon farko, yayin da wasu kamfanoni da hukumomi kusan 200 suke halartar bikin a tsawon shekaru 9 a jere.
Baje kolin dake gudana cikin shekaru 9 a jere, ya nuna wa kasashen duniya cewa, kasar Sin ita ce masanaantar kasa da kasa, kuma kasuwar kasa da kasa, wadda ke kan gaba a fannin sayar da kayayyaki, tana kuma kan gaba a fannin shigo da hajoji.
A tsawon shekaru 17 a jere, kasar Sin ta ci gaba da kasancewa kasuwa ta biyu mafi girma a duniya wajen shigo da kaya, kuma muhimmiyar abokiyar ciniki ga kasashe da yankuna sama da 160, a cikin rubui uku na farkon bana, inda yawan kayayyakin da Sin ta shigo da su ya karu da kaso 22.3 cikin dari, idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata.
Shirin shekaru biyar-biyar na bunkasa tattalin arziki da zamantakewar kasar Sin na 15, ya jaddada muhimmancin inganta ci gaba mai daidaito, a fannin shigo da kaya da fitar da su zuwa kasashen waje, tare da ba da shawarar “ci gaba da gudanar da bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin ko CIIE cikin nasara.
Wannan mataki zai inganta bude kasuwanni, tare da bai wa duniya damar cin gajiyar damammakin da ake samarwa yadda ya kamata. (Mai Fassara: Maryam Yang)













