A ranar Juma’a 6 ga wata ne aka gudanar da taron tattaunawa na duniya, kan Salon Shugabancin kasar Sin da Ci Gaban Duniya, wanda Babban Rukunin Gidajen Rediyo da Talabijin na Sin (CMG), da hadin gwiwar ofishin jakadancin Sin a Ghana suka shirya a birnin Accra.
Shugaban CMG Shen Haixiong, ya gabatar da jawabi ga taron ta kafar bidiyo. Kana, jakadan kasar Sin dake kasar Ghana Cong Song, da ministar yawon bude ido, raya al’adu da fasahohin kirkira ta kasar Ghana Abla Dzifa Gomashie suka halarci bikin tare da gabatar da jawabai.
Kusan baki 150, wadanda suka fito daga fannonin siyasa, da ilimi, da kafofin watsa labarai tare da kungiyoyin farar hula na kasar Ghana, sun gudanar da tattaunawa mai zurfi game da yadda “Salon Shugabancin kasar Sin” zai iya taimakawa kasashe masu tasowa.
Cikin jawabinta, Abla Dzifa Gomashie ta ce, wannan tattaunawa ta zama muhimmin dandamali ga dukkan bangarorin, domin nazarin alakar da ke tsakanin dorewar tsare-tsare da ingantaccen shugabanci, da dauwamammen ci gaba.
Haka kuma ta taimaka wajen gano sabbin damammaki ga kasar Ghana, domin zurfafa hadin gwiwarta da kasar Sin a fannonin shugabancin kasa, da ci gaban tattalin arziki, da mu’amala tsakanin al’ummomin kasashen biyu.
Haka zalika, ta ce sashen kirkire-kirkire da swuka shafi yada al’adu, da yawon bude ido, na da damar zama sabon ginshikin hadin gwiwa tsakanin Ghana da Sin. Har ila yau, bangarorin biyu za su iya zurfafa hadin gwiwarsu, a fannoni kamar zuba jari a bangaren al’adu da yawon bude ido, da kare kayan tarihi da al’adun gargajiya, da kuma bunkasa kwarewar kwararru, domin neman ci gaba mai dorewa. (Mai Fassara: Maryam Yang)













