Ya zuwa yanzu, wakilai daga kasashe da yankuna gami da kungiyoyin kasa da kasa 145 ne suka nuna sha’awarsu ta halartar bikin baje kolin kasa da kasa na kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin (CIIE) da za a gudanar a birnin Shanghai, kamar yadda masu shirya bikin suka bayyana Talatar nan.
Mataimakin darektan ofishin CIIE Sun Chenghai, ya bayyana a yayin taron manema labaran da aka shirya cewa, kamfanoni 284 da ke kan gaba a harkokin masana’antu, ciki har da wasu manyan kamfanoni 500 dake sahun gaba a duniya, za su halarci bikin baje kolin na wannan shekara. (Mai fassarawa: Ibrahim daga CMG Hausa)