A kan ce “A mai da hankali kan aikace-aikacen wani, maimakon maganarsa”. Yayin da ake tantance aikin gwamnati ma, haka abun yake. Idan wata gwamnati ta iya cika alkawarin da ta dauka, to, jama’a za su amince da ita, sa’an nan za a samu damar gudanar da harkokin mulki yadda ake bukata.
A yau lahadi, firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya gabatar da rahoton ayyukan gwamnati a gun taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin. Idan an kwatanta rahoto na wannan shekara, da na bara, za a fahimci yadda gwamnatin kasar ta yi kokarin cika alkawari a shekarar 2022.
In mun duba fannin samar da guraben aikin yi, gwamnatin kasar Sin ta yi shirin samar da guraben aikin yi ga karin mutane fiye da miliyan 11 a shekarar 2022, daga baya a hakika ta samar da guraben aikin yi miliyan 12 da dubu 60. A fannin farashin kayayyaki, kasar ta yi shirin kayyade karuwar farashin kayayyaki cikin kashi 3%. Daga bisani ta samu karuwar da ba ta wuce kashi 2% ba. Sa’an nan a fannin samar da hatsi, da ma gwamnatin kasar ta yi shirin samar da hatsin da yawansa ya wuce kilo biliyan 650, inda adadi na hakika da ta samu ya kai kimanin kilo biliyan 686.6.
Wadannan jimiloli sun nuna cewa gwamnatin kasar Sin ta cimma burikan da ta sanya a fannoni daban daban. Ban da jimilar GDP, wadda ta yi shirin samun karuwarta ta kashi 5.5%, amma hakikanin karin da ta samu ya kasance kashi 3%. Sai dai wannan batu ba wani abu mai wuyar fahimta ba ne, saboda annobar cutar COVID-19, da yakin da ake yi tsakanin Ukraine da Rasha, da yadda kasar Amurka ta sa ruwan kudin ajiya a bankunanta ya karu, wadanda duka suka haifar da matsala ga tattalin arzikin duniya. Ta yin la’akari da wannan yanayin da ake ciki, karuwar da tattalin arzikin Sin ya samu ba wani abu mai sauki ba ne, kana tana kan gaba a duniya wajen kiyaye karuwar tattalin arziki.
Rahoton da Li ya gabatar, ya kuma shafi yadda kasar Sin ta yi kokarin zamanintar da kai cikin shekaru 5 da suka wuce, inda ta daidaita matsalar talauci daga tushenta, da kare wata matsakaiciyar karuwar GDP ta kashi 5.2%, da samun karuwar bangaren masana’antu mai alaka da fasahohin zamani da ta kai kashi 10.6%, da sanya tsawon layin dogon jirgin kasa mai saurin gudu karuwa daga kilomita dubu 25 zuwa kilomita dubu 42, da dai sauransu. Ta yin la’akari da wadannan nasarorin da aka samu, ba za a yi mamaki ba ganin burin raya kasa da gwamnatin kasar Sin ta gabatar ma majalisar wakilan jama’ar kasar a matsayin shawara, wanda ya hada da neman samun karuwar GDP kimanin kashi 5%, da samar da sabbin guraben aikin yi ga karin mutane miliyan 12, da dai makamantansu. Domin wannan buri bai wuce matsakaiciyar karuwar da tattalin arzikin Sin ya samu cikin shekaru 5 da suka wuce ba.
Cikin shekarar 2022 da ta gabata, na taba gamuwa da mutane da yawa, wadanda annobar COVID-19 ta yi tasiri kan zaman rayuwarsu, a birnin Beijing. Cikinsu akwai mai kantin sayar da kofi, wanda harkar kantinsa ta gamu da matsala, da mai jigilar kaya, wanda ya ci gaba da aiki har zuwa tsakar dare, da mai yi wa mutane masu yawon shakatawa jagora, wanda ya fara wani aiki na daban na wucin gadi. Sai dai na ga akwai wasu abubuwa na bai daya a cikin zukatansu, wato hakuri da fara’a: Sun yarda cewa duk wata matsala, za a ga bayanta, kana nan gaba za a samu makoma mai haske. To me ya sa suke da wannan imani? Saboda sun dade suna shaidawa da idanunsu, yadda kasarsu ta samu nasarar daidaita matsaloli daban daban, da cika dukkan alkawuran da ta yi.
Sai wata gwamnati ta cika alkawarinta, sannan jama’a za su amince da ita, sa’an nan muddin jama’a sun yarda da gwamnati, to, za a samu damar aiwatar da matakan raya kasa yadda ake bukata. Saboda haka, ana iya ce, cika alkawari tushe ne ga aiwatar da mulki ta wata nagartacciyar hanya. (Bello Wang)