ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yunkurin Tauye Ci Gaban Fasahar Kera “Chips” Ta Sin Ba Zai Haifar Da Da Mai Ido Ba

by CGTN Hausa and Sulaiman
1 year ago
Chip

A baya bayan nan, gwamnatin Amurka ta dauki wasu matakai na kokarin matsa lamba ga wasu kasashe, don tabbatar da cewa ba su rungumi kayan hada na’urorin laturoni na “Chips” da kasar ke kerawa ba, ciki har da samfurin “Ascend” da katafaren kamfanin fasahohi na Huawei ke kerawa, wanda hakan a zahiri ke shaida yunkurin Amurka na aiwatar da fin karfi, da baiwa kasuwanninta kariya.

Duk da cewa Amurka ta bayyana matakin a matsayin na tsaron kasa, a daya hannu masharhanta na ganin hakan ya sabawa ka’idar adalci ta kasuwanci, zai kuma yi mummunan tasiri ga ci gaban fasahohin sadarwa. Kazalika, matakin na Amurka ba zai dakile ci gaban da Sin ke samu a fannin ba, sai dai ma ya gurgunta tsarin samarwa, da rarraba hajoji masu nasaba da fasahohin sadarwa tsakanin sassan kasa da kasa, da hana kasashen duniya cikakkiyar dama ta zabar hanyarsu ta gina fasahohin sadarwa, da fasahar AI bisa hakikanin bukatunsu.

  • An Kashe ‘Yan Ta’adda 6,260, An Ceto Mutane 5,365 Acikin Shekaru Biyu – Hedikwatar Tsaro 
  • Daga Xi’an Zuwa Astana: Me Muka Koya Daga Taron Kolin Sin Da Kasashen Tsakiyar Asiya

Duk da matakan na Amurka, a halin da ake ciki kamfanonin Sin masu kera nau’o’in “chips” a cikin gida na ta karuwa, inda kamfanoni irin su Huawei, da Biren, da Enflame, da YMTC ke kan gaba wajen samun manyan nasarori a fannin.

ADVERTISEMENT

Kasuwar “chips” ta Sin a fannin fitar da kayayyaki ta bunkasa, daga darajar da ta kai yuan biliyan 559.1 a shekarar 2018, zuwa sama da yuan tiriliyan 1.1 a shekarar 2024 da ta gabata. Bugu da kari, duk da koma baya na dan lokaci da fannin ya gamu da shi sakamakon yunkurin danniya na Amurka, akasarin kamfanonin fasahohin sadarwa na Sin sun jure wannan yanayi tare da kara karfafuwa, har ma wasu sun kai ga gina nasu manhajojin sarrafa na’urori masu kwakwalwa bisa fasahohin kashin kai.

Tabbas, bai dace batun tsaron kasa ya zama makamin dakile harkokin samar da ci gaba ba. Manufofi dake haifar da wariya, da mamaye kasuwar wasu kasashe na da matukar illa, domin kuwa suna iya gurgunta daidaito, da aminci da ake bukata a fannin bunkasa fasahohin zamani. A daya hannun, manyan damammaki da sassan kasa da kasa za su ci gajiyarsu, za su tabbata ne kadai idan an yi hadin gwiwa a fannin kirkire-kirkire, maimakon kafa shingaye barasa amfani ga kowa.

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Chip
CGTN Hausa
+ posts Bio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/

    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa
Chip
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi
  • Sulaiman
    Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

MASU ALAKA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
Daga Birnin Sin

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
Daga Birnin Sin

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi
Daga Birnin Sin

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Next Post
Xi Ya Tattauna Da Shugaban Rasha Ta Wayar Tarho

Xi Ya Tattauna Da Shugaban Rasha Ta Wayar Tarho

LABARAI MASU NASABA

Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.