SHAIKH DAHIRU USMAN BAUCHI dai fitattacen malami ne a Nijeriya kuma babban jigo a Darikar Tijjaniyya da ya yi fice ba ma a Nijeriya kadai ba, har a cikin wasu sassan duniyar nan. Da yake ya cika shekara 100 da haihuwa a bana a ranar Litinin da ta gabata, 2 ga Muharram, 1446 bayan hijirah, KHALID IDRIS DOYA ya kawo mana wata hira da aka taba yi da shi wanda kusan ya bayyana komai na rayuwarsa har adadin ‘ya’ya, jikoki, mata, da kuma abun da yafi so da abun da ba ya so. Ga cikakkiyar hirar:
Ko Shaihi za ka fara da gabatar da tarihinka?
Assalamu Alaikum wa Rahambatullahi. Tarihina dai ni Bafulatani ne, dukkanin Kakannina hudu Fulani, domin kowani mutum yana da Kakani hudu a rayuwa, ta wajen Babansa biyu, ta wajen Mamansa biyu dukkaninsu Fulani ne. To ni dukkanin kakanina Fulani ne babu inda muka hadu da wata kabila ta kowace fuska. Mu Fulanin Bauchi ne a lokacin da Bauchi take hade da Gombe. Idan kuma aka raba Bauchi da Gombe, to mu Fulanin Bauchi ne, a lokaci guda kuma mu Fulanin Gombe ne. Ta wajen ubana ni bafulatanin Bauchi ne, ta wajen uwata ni bafulatanin kauyen Nafada ne da ke can Gombe. An haifeni a alif da 1927 a cikin watan Junairu wanda yayi daidai da alif 1346 a cikin watan Muharram a ranar laraba aka haifeni.
Kuma Babana sunansa Alhaji Usman dan Alhaji Adam mahaddaci ne, ni na rayu ne a hanunsa na haddace Alkur’ani ne a hanunsa. Sunan mahaifita Hajiya Maryam. Daga baya ne kuma aka tura ni dunya domin na je na gyara tilawata. Na shiga duniyar na kuma gyara tilawar tawa har ma ana fada min Gwani, suna kira na kuma Gangaran a fagen haddar Alkur’ani mai girma. A bisa haka ne ma ya ce zai turani duniya na je na sake nemo ilimi, ya turani nan Bauchi domin neman ilimi. Na fara neman ilimi ban riga na samu ilimin da yawa ba sai Allah ya sa harkar Shehu Ibrahim Kaulaha din nan ta tashi. Daman shi baban nawa dan Tijjaniyya ne Mukaddami ne ta sarsalar Umaru Futi wato Muhammadu Ghali, muna ciki wannan gwagwarmaya ne kuma shi ne kuma ya ba ni Darikar Tijjaniyya, a wajensa na haddace karatun Kur’ani kuma a wajensa na karbi darikar Tijjaniyya shi Alhaji Usman din (mahaifina kenan). Bayan da muka shiga harkar Shehu Ibrahim din nan sai ya zama kowace harka nawa sai ta hada da maganar Shehu Ibrahim. Alhamdu llahi na samu rabo mai tarin yawa a sha’aninsa, na soma yin tafsiri kusan a shekara ta alif 1950 da wani abu haka (kusan haka ne). Sannan Na yi aure a alif 1948 aure na fari, a wannan shekarar na yi.
Cikin alherin da Allah ya yi mini ‘ya’yana tun suna kanana suke haddace Kur’ani, a da ‘ya’yana suna haddace Kur’ani a lokacin da suke da shekara 11, har aka dawo 10, aka zo tara har muka dawo muka samu yanzu akwai ‘ya’yana da suka haddace Kur’ani suna da shekara bakwai-bakwai da haihuwa a duniya.
Kamar gabaki daya za a iya cewa ‘ya’yan Malam su nawa ne kuma jikokinka nawa ne?
Alhamudullahi suna da dama (dariya sosai).
Ka bayyana cewar kana da kakanin biyu daga Gombe a halin yanzu, biyu daga Bauchi. Ainihi takamaimai kai a ina aka haife ka?
Kasan mu Fulani dan fari a gidan uwarsa ake haifansa, sabili da haka ni an haife ni ne a garin Nafada garin uwata din kenan, a wannan garin na Nafada aka haifeni.
Allah shi gafarta Malam matanka nawa ne?
Matana hudu (4) ne na kuma dade ina tare da mata hudu din nan, wadansu sukan tsufa sai su yi ritaya da kansu sai kuma na sake samun wadansu matan. Matana hudu ne a halin yanzu.
Yanzu idan aka dubi karatunka na addini wani bangare ne ka fi kwarewa?
Na farko bangaren da na fi kwarewa sosai a kai ita ce sana’ata, shi ne Alkur’ani. Daga nan kuma ta bangaren tafsirin nan nan malaman tafsiri sun ce lallai na iya tafsiri in ji su. A cikin abubuwan da na fi kwarewa Kur’ani, tafsiri sai kuma bangaren Ma’arifa. Ma’anar Ma’arifa shi ne ilimin zuciya wanda ake kiransa ilimin tarbiyya, mukashafa nan ma masu shi sun ce na sa shi, Shehu Ibrahim ya ce lallai na san wannan bangaren. Sauran ilimomi ina tattabawa su hadisi, lugga, li’irabi, tasrifi, su fikiho duk ina tattabawa.
Masu sauraron tafsirinka suna ganin idan aka yi maka tambaya a lokacin da kake tafsiri kana fakewa bada amsa ne da bada misali mai makon kai tsaye mene ne hikimar yin hakan?
Wato shi buga misali wani runduna ne na Allah mai shigar da ilimi cikin kawunan mutane, idan ka kawo amsar magana sai ka buga misalin da za ta hau kan mutane domin fahimtar da su. Shi buga misali yana jawo hankali a fahimci mene ne aka fada. Misali na da makukar muhimmaci wajen bada amsa.
Ko ka yi karatun boko, in ka yi a wace marhala ka tsaya?
(Dariya) ai ko ABCD ban yi ba. Ni ban yi karatun boko ba, ko ABCD ban je na yi ba ni.
Ba ka yi karatun Boko ba, yaya ake gwawarmayar rayuwa ta zamanin yau?
Eh to da yake muna tare da masu bokon, masu karatun na boko, wasu ‘ya’yanmu sun zama Daktoci ba daya ba ba biyu ba, Don haka suna dafawa wajen tafiyar da komai yanda ya dace. Muna da masu karatun Boko sosai a cikin ‘ya’yana da almajiraina kuma muna tare da su, ta haka muke gwagwarmayar rayuwar yau din.
Menene ya fi baka sha’awa a rayuwarka?
Abun da ya fi bani sha’awa irin yanda na maida Kur’ani sa’anata da kuma Darikar Tijjaniyar nan yanda na rungume ta ta zama rayuwata, kuma da dukkanin wani mutumin da yake dangantuwa da son Annabi da son Allah ina sha’awar in sadu da shi.
Kamar misali a lokacin da baka karatun Alkur’ani me kake yi a lokacin da kake hutun?
Wai a lokacin da nake hutu ina shagaltuwa ne da karanta Salatil Fatihi, da Tasbihi da kuma Istigfari da salatin Annabi da sauran zikiri. Na kan shagulta da zikirori ne a lokacin da na ke hutawa.
Shehu Dahiru wani abinci ka fi sha’awa a rayuwarka?
(Cikin dariya sosai ya amsa mana da cewa) abincin Hausawa da Fulani so na ke sha’awa, ina cin tuwon shinkafa, ina cin shinkafar da ita kanta. To amma a yanzu a halin da muke ciki na daina cin dawa na daina cin masara na kuma daina cin tuwon masara da tuwon gero dukka na daina cin su yanzu, kuma babu wani likitan da ya hanani cinsu hankali na ne kawai ya kisu. Ka ga yanzu dai ina cin tuwon shinkafa, shinkafar da kanta. Masara, tuwon masara, Dawa, tuwon gero dukka na yi ritaya da cinsu a halin yanzu bana cinsu bisa ra’adin kaina.