• English
  • Business News
Tuesday, November 11, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Cikar MDD Shekara 80: Nasarorinmu Sun Kara Mana Kaimi Da Kyakkyawar Makoma A Nan Gaba

by Rabi'u Ali Indabawa and Sulaiman
4 months ago
MDD

Shekara 80 da suka gabata a makamanciyar wannan rana, an rattaba hannu kan Yarjejeniya ta Majalisar Dinkin Duniya (MDD) a San Francisco, inda aka sauya tsari na yaki da duniya ta fuskanta shekaru da dama zuwa samar da kyakkyawar makoma. Tsawon shekaru 80, MDD ta tsaya a matsayin mai bayyana fatanmu na hadin gwiwar kasa da kasa, mai bayyana ma’anar burinmu na kawo karshen “cutarwa a yaki.” A cikin wannan duniyar da ke cike da son zuciya, wannan muhimmin mataki ne da ya dace a dauka.

MDD ta kasance kungiya daya tilo da bata da tamka, kuma ita kadai ce ta dawwama. Wannan tsayin daka yana da ban mamaki idan muka yi la’akari da yanayin kafuwarta.

  • An Sauya Sunan Makarantar Wasanni Don Girmama Ƴan Kano Da Suka Yi Hatsari
  • Gwamna Yusuf Ya Jagoranci Tawagar Kano Zuwa Jana’izar Marigayi Aminu Dantata A Madina

Babu wata kungiya da za a ce ba ta da aibi. Amma domin a bayyana kokarin Sakatare-Janar dinta na biyu, Dag Hammarskjöld: An kafa MDD ba don daukaka dan’Adam ba sai don cetonmu daga mawuyacin hali, kuma ba za ta gaza a kan wannan manufa ba.

LABARAI MASU NASABA

Nakasa A Mahangar Karin Magana: Guzurin Ranar Nakasassu Ta Duniya

Khalifan Sheikh Ibrahim Inyas Daga Ƙasar Sanigal Ya Goyi Bayan Sunusi Lamido Sunusi II

Muna sane da wuraren da ake yaki masu taba zuciya: Gaza, Sudan, Ukraine da sauran wurare. Rikicin baya-bayan nan tsakanin Iran da Isra’ila, wani abin tunatarwa ne ga raunin zaman lafiya musamman a yankin Gabas ta Tsakiya mai fama da tashe-tashen hankula.

Duk da haka, a cikin wannan tashin hankali, mun yi nasarar dakile yakin duniya na uku. A wannan zamani na nukiliya, wannan nasara ce da ba za mu taba dauka da wasa ba. Ita ce wacce ta kamata mu kiyaye da karfin kokarinmu.

A cikin shekaru 80 da suka gabata, yawancin ci gaban dan’Adam shi ma yana da tasiri a MDD kai tsaye. Yi la’akari da nasarar da aka samu ta ci gaban karni, wanda kasashe mambobi 189 suka karba a cikin kasashe 2000 da kari.

Fiye da kungiyoyin kasa da kasa 20 ne suka ba duniya taswirar hanya daya domin daukar mataki.

A 2015, idan aka kwatanta da 1990, matsanancin talauci ya ragu sama da rabi. Mutuwar yara ta ragu da kusan kashi 50 cikin dari. Kuma miliyoyin yara musamman ‘yan matan da ake dannewa hakki sun shiga makaranta a karon farko.

Akwai wani muhimmin labarin ci gaba, wanda ba a mantawa da shi, shi ne wargaza daula. Shekaru 80 da suka gabata, mulkin mallaka ya yi shuhura a duniya. A yau, fiye da 80 da aka yi musu mulkin mallaka a fadin Asiya, Afirka, Caribbean, da Pacific sun sami ‘yancin kai kuma sun shiga MDD. Wannan canji da wannan Kungiya ta goyi baya kuma ta halalta shi ya sake fasalin tsarin duniya.

Shiga Tsakani domin samar da ci gaba

Duniya ta canza sosai tun daga 1945. A yau, kungiyar na fuskantar matsalar karancin kudi. Duk da alkawalin da aka yi na 2030 don samar da ci gaba mai dorewa, ci gaban kuma bai daidaita ba. Daidaiton jinsi ya kubuce mana. Alkawarin da muka yi na takaita hauhawar dumamar duniya da kare duniyarmu ya karanta.

Wadannan koma baya ba sun haifar da raguwar buri amma su ne manyan kudurorinmu. Majalisar Dinkin Duniya na nuna kimarta a lokutan rikici. Wadanda suka kafa ta sun shaida dan’Adam a matsayin mafi barna kuma ba su yanke kauna ba, saboda karfin hali. Dole ne mu zayyana wadannan nasarori.

Yayin da muke bikin wannan zagayowa, dole ne mu sake farfado da kiran hadin kai da aka yi daga San Francisco shekaru 80 da suka gabata.

Mun gina tsarin duniya farat daya, domin rushe tsarin yaki. Mun yi hakan ne da hangen nesa cikin gaggawa. Yanzu kuma, mun sami kanmu a lokacin sakamako. Hadarin yana da yawa. Haka zalika kuma karfinmu na yin aiki na da yawa.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Nakasa A Mahangar Karin Magana: Guzurin Ranar Nakasassu Ta Duniya
Muƙala

Nakasa A Mahangar Karin Magana: Guzurin Ranar Nakasassu Ta Duniya

December 3, 2024
Khalifan Sheikh Ibrahim Inyas Daga Ƙasar Sanigal Ya Goyi Bayan Sunusi Lamido Sunusi II
Al'adu

Khalifan Sheikh Ibrahim Inyas Daga Ƙasar Sanigal Ya Goyi Bayan Sunusi Lamido Sunusi II

May 27, 2024
Zan Goyi Bayan Peter Obi A 2027 Matsawar PDP Ta Sahale Masa Yin Takara – Atiku
Muƙala

Zan Goyi Bayan Peter Obi A 2027 Matsawar PDP Ta Sahale Masa Yin Takara – Atiku

May 19, 2024
Next Post
Yaushe Za A Dakatar Da Yi Wa `Yan Arewa Kisan Gilla?

'Yan Bindiga Sun Sake Kai Hari Kan Al’ummar Benuwe, Sun Kashe ‘Yansanda 4

LABARAI MASU NASABA

An Daddale Kulla Cinikin Sama Da Dala Biliyan 83 A Bikin CIIE Na Kasar Sin 

An Daddale Kulla Cinikin Sama Da Dala Biliyan 83 A Bikin CIIE Na Kasar Sin 

November 10, 2025
Kamfanonin Kasa Da Kasa Na Fatan Yin Amfani Da Damammaki Na Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar–Biyar Karo Na 15 Na Sin

Kamfanonin Kasa Da Kasa Na Fatan Yin Amfani Da Damammaki Na Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar–Biyar Karo Na 15 Na Sin

November 10, 2025
Ƴan Bindiga Sun Sace Mata 4 Masu Shayarwa, Da Shanu 50 A Kano

Ƴan Bindiga Sun Sace Mata 4 Masu Shayarwa, Da Shanu 50 A Kano

November 10, 2025
Sin Ta Dakatar Da Jiragen Ruwan Amurka Daga Biyan Kudi Na Musammam A Tashoshinta Na Ruwa

Sin Ta Dakatar Da Jiragen Ruwan Amurka Daga Biyan Kudi Na Musammam A Tashoshinta Na Ruwa

November 10, 2025
Sin Ta Harba Sabon Rukunin Taurarin Dan Adam Masu Zagaye Kusa Da Doron Kasa

Sin Ta Harba Sabon Rukunin Taurarin Dan Adam Masu Zagaye Kusa Da Doron Kasa

November 10, 2025
Babban Dalilin Da Ya Sa EFCC Ke Naman Tsohon Minista Ruwa A Jallo

Babban Dalilin Da Ya Sa EFCC Ke Naman Tsohon Minista Ruwa A Jallo

November 10, 2025
Binciken Ra’ayin Jama’a Na CGTN: Ci Gaba Da Bude Kofa Mai Zurfi A Sin

Binciken Ra’ayin Jama’a Na CGTN: Ci Gaba Da Bude Kofa Mai Zurfi A Sin

November 10, 2025
Gwamnati Ta Nemi Ƴan Nijeriya Su Ƙwantar Da Hankali Kan Barazanar Trump

Gwamnati Ta Nemi Ƴan Nijeriya Su Ƙwantar Da Hankali Kan Barazanar Trump

November 10, 2025
Mataimakin Firaministan Kasar Sin Zai Ziyarci Kasashen Guinea Da Saliyo

Mataimakin Firaministan Kasar Sin Zai Ziyarci Kasashen Guinea Da Saliyo

November 10, 2025
FCT Ta Saka Ranar 1 Disamba Don Kammala Biyan Kudin Hajjin 2026 N7.7m

FCT Ta Saka Ranar 1 Disamba Don Kammala Biyan Kudin Hajjin 2026 N7.7m

November 10, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.