Dokar tabbatar da karuwar tattalin arziki da damar raya nahiyar Afirka (AGOA) muhimmiyar doka ce ta kasar Amurka, a fannin samar da gatancin ciniki ga kasashen Afirka. Kana an dade ana kallonta a matsayin tushen huldar Afirka da Amurka ta fuskar tattalin arziki. Amma a ranar 30 ga watan Satumban da ya gabata, wa’adin dokar ya cika, ko da yake dimbin kasashen dake nahiyar Afirka sun yi ta kira da a tsawaita wa’adin dokar. Wannan batu ya nuna ra’ayin kasar Amurka dangane da kasashen Afirka, wato ko-in-kula.
A shekarar 2000, gwamnatin Bill Clinton ta sa aka zartas da dokar AGOA da zummar zurfafa alakar ciniki tsakanin kasar Amurka da kasashen Afirka dake kudu da hamadar Sahara. Wannan doka ta shafi kasashe 32, inda aka ba su damar fitar da nau’ikan kayayyaki fiye da dubu daya zuwa kasar Amurka. Sa’an nan a shekarar 2023, wato shekara ta karshe da ake iya samun alkaluma masu nasaba da dokar, kasashen Afirka sun fitar da kayayyakin da darajarsu ta kai dalar Amurka biliyan 9.7 zuwa kasar Amurka, bisa sharadin gatanci da aka tanada cikin dokar AGOA.
Sai dai bayan da shugaba Donald Trump ya hau karagar mulkin kasar Amurka a farkon bana, yanayi ya sauya: An fara karbar karin harajin kwastam kan kayayyakin kasashen Afirka da ake shigar da su kasar Amurka, da rufe hukumar samar da agaji a duniya ta kasar Amurka ta USAID, gami da barin wa’adin dokar AGOA ta cika ba tare da tsawaita shi ba a wannan karo. A hannu daya, kasar Amurka ta janye gatanci da tallafin da ta ba kasashen Afirka a baya, kana a dayan hannun, tana neman samun karin kudi daga wajensu, hakan ya kara raunana ayyukan masana’antun Afirka wanda ko da ma ba su da karfi. Bisa gargadin da hukumar kula da ciniki da ci gaban tattalin arziki ta Majalisar Dinkin Duniya (UNCTAD) ta gabatar a kwanan baya, rashin aikin dokar AGOA zai haddasa raguwar kayayyakin da ake fitar da su daga kasashen Afirka zuwa kasar Amurka sosai, musamman ma a kasashen Kenya, da Tanzania, da Madagascar, da dai sauransu.
Yanzu haka, wasu shugabannin kasashen Afirka na kokarin lallashin masu fada-a-ji na kasar Amurka don su taimaka wajen tabbatar da tsawaitar wa’adin dokar AGOA. Kana wani jami’in fadar White House ta kasar Amurka shi ma ya ce akwai yiwuwar kara wa’adin da shekara daya. Sai dai karin harajin fito da kasar Amurka ta saka ma kayayyakin dimbin kasashen dake nahiyar Afirka ya riga ya kawar da ma’anar gatancin da dokar AGOA ta kunsa. Ban da haka ana shakku kan ko gwamnatin Trump na da sahihanci wajen tsawaita wa’adin dokar AGOA. A cewar Farhana Paruk, masaniyar ilimin al’amuran kasa da kasa ta kasar Afirka ta Kudu, gwamnatin Trump ka iya amfani da batun wajen matsawa kasashen Afirka lamba, don neman biyan bukatarta ta fuskar harkokin siyasa.
A zahiri, ra’ayin gwamnatin kasar Amurka na yanzu dangane da kasashen Afirka, ya kara zama na ko-in-kula, idan an kwatanta shi da na gwamnatin kasar na lokacin baya. Dalilin da ya sa ake samun wannan sauyi, shi ne raguwar karfin kasar Amurka, da tasirinta a duniya. A baya, kasar dake da imani kan makomarta ta iya samar da moriya ga sauran kasashe, don musayar goyon bayansu. Amma a zamanin yanzu, kasar Amurka tana kallon sauran kasashe a matsayin “masu samar mata da jini”, inda take lura da moriya ta gajeren lokaci kawai, maimakon adalci da abokantaka. (Bello Wang)