A ƙalla jami’an tsaro 53 aka kashe a faɗin Najeriya cikin makonni biyu da suka gabata, bisa ga ƙididdigar da Daily Trust ta tattara daga rahotannin kafafen watsa labarai. Waɗanda aka kashe sun haɗa da Sojoji, da ƴansanda, da jami’an NSCDC, da na shige-da-fice da na haraji, da kuma na sa-kai, da mambobin JTF da ƙungiyoyin tsaron al’umma na jihohi. Wannan adadi bai haɗa da rahotannin da ba a bayar ba.
Yawancin jami’an an kashe su ne yayin da suke amsa kiran kai hari kan al’umma, yayin da wasu kuma aka yi musu kwanton ɓauna a wuraren binciken ababen hawa da sansanonin tsaro. Manyan hare-haren kwanan nan sun faru ne a jihohin Biniwe da Kogi, inda ƴan bindiga suka hallaka jami’an ƴansanda bakwai da wasu jami’an tsaro a hare-hare dabam-dabam tsakanin Juma’a da Lahadi. Haka kuma an yi garkuwa da wasu jami’an a lamarin da ya auku a Binuwe
- Ƴan Bindiga Sun Yi Wa 9 NSCDC Ƙwantan Ɓauna A Binuwe
- Wasu ‘Yan Ta’adda Dauke Da Makamai Sun Harbi Limamin Katolika A Binuwe
Waɗannan kashe-kashen sun ƙara haskaka yadda barazanar tsaro ke ta ƙara jawo asarar rayukan jami’an tsaro a Nijeriya. Binciken da Daily Trust ta gudanar a watan Disambar 2024 ya nuna cewa an kashe a ƙalla ƴan sanda 229 daga Janairu 2023 zuwa Oktoba 2024 sakamakon hare-haren ƴan bindiga, da na masu tada kayar baya, masu al’ada da kuma ƴan fashi da makami. Sabbin hare-haren sun nuna cewa tashin hankali na ƙaruwa duk da yunƙurin samar da tsaro da ake ci gaba da gudanarwa.
A martanin Hukumar DSS, ta gurfanar da mutane tara a gaban Babbar Kotun Tarayya a Abuja a makon jiya kan zargin hannu a kisan da aka yi kwanan nan a jihohin Binuwe da Filato. Cikin waɗanda aka gurfanar har da Haruna Adamu da Muhammad Abdullahi daga Jihar Nasarawa, bisa zargin hannu a kisan gilla da aka yi a Guma LGA ta Benue.
Haka kuma an gurfanar da Terkende Ashuwa da Amos Alede bisa zargin ramuwar gayya da ta haddasa lalata kadarori da rasa shanu 12 a ƙauyen Ukpam. DSS ta kuma gurfanar da wani mutum daban kan mallakar bindigogi M16 guda bakwai ba bisa ƙa’ida ba.