Minista mai kula da masana’antu, ciniki da zuba jari ta kasar Najeriya, Jumoke Oduwole, ta fada a jiya Lahadi cewa, matakin karbar karin harajin kwastam da kasar Amurka ta yi shirin dauka, zai yi mummunan tasiri kan fitar da kayayyakin Najeriya zuwa kasar Amurka, da lalata huldar ciniki dake tsakanin kasashen 2.
Hakika yawan harajin kwastam na kaso 14% da kasar Amurka za ta kakaba wa kasar Najeriya bai kai adadin harajin da Amurka din ta sanya wa sauran kasashe dake nahiyar Afirka ba, idan an kwatanta da kaso 47% na kasar Madagascar, da 40% na Mauritius, da 37% na Botswana, da 30% na Afirka ta Kudu, da dai sauransu. Kana abun mamaki shi ne, kasar da Amurka za ta karbi mafi yawan haraji bisa kayayyakinta a nahiyar Afirka ita ce Lesotho, ko da yake karamar kasa ce mai fama da koma bayan tattalin arziki, inda yawan harajin da Amurka za ta kakabawa kasar zai kai kaso 50%.
- INEC Ta Musanta Korar Farfesa Yakubu A Matsayin Shugaban Hukumar
- Harin Filato: An kashe Mutane 40, An Kona Gidaje 383, Fiye Da Mutane 1,000 An Raba Su Da Muhallansu
Da ma dokar Amurka ta tabbatar da ci gaban kasashen Afirka (AGOA) ta ba wasu kasashen dake nahiyar Afirka damar fitar da kayayyakinsu zuwa kasar Amurka, ba tare da bukatar biyan harajin kwastam ba. Amma yanzu, matakin karbar karin haraji da kasar Amurka ta shirya dauka ya nuna cewa za a ga bayan dokar nan ta AGOA. A cewar wani shahararren lauya na kasar Birtaniya mai suna Colette Ven, matakin kasar Amurka tamkar yanke hukunci ne kan kasashen Afirka, bisa ribar da suka taba samu sakamakon dokar AGOA din.
Ban da haka, a ganin masana na kasashe daban daban, munufar haraji ta kasar Amurka ta keta ka’idojin kungiyar ciniki ta duniya WTO, da bijirewa bambancin karfin tattalin arziki na kasashe daban daban. Inda kasar take neman cin zalin kasashen duniya, da hana ci gaban tattalin arzikin kasashe masu tasowa.
A nata bangare, ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ita ma ta sanar da cewa, kowace kasa na da hakkin neman ci gaba, saboda haka bai kamata a ba wasu kasashe damar yin babakere ba. Ganin yadda kasar Amurka ke neman dora moriyarta a kan hakkin kasashen duniya, ya sa kasar Sin kin amincewa da matakinta.
Yanzu haka ra’ayin kasar Sin na samun amincewa daga mutanen kasashe daban daban. Bisa sakamakon binciken ra’ayin jama’a da kafar watsa labarai ta kasar Sin CGTN ta gudanar, cikin mutanen kasashe daban daban da aka yi musu tambayoyi, kaso 86.9% sun ce matakan ramuwar gayya da kasashe daban daban suka dauka bisa matakin karbar karin haraji na kasar Amurka, sun halatta, kana kaso 87.7% na mutanen sun ce ya kamata kasashe daban daban su yi hadin gwiwa, a kokarin dakile matakin Amurka na cin zarafin sauran kasashe.
A nahiyar Afirka ma, matakin Amurka ya janyo sabon tunani kan dabarar raya kasa. Inda masanin ilimin shari’a na kasar Najeriya Livingstone Wechie ya ce, ko da yake kasar Amurka ta taba alkawarin raya masana’antu a kasashen Afirka karkashin dokar AGOA, sakamako na karshe ya nuna cewa ta yi karya ke nan. Saboda haka mista Wechie ya ce dogara kan tallafin da ake samu daga kasashen waje ba zai raya tattalin arzikin kasashen Afirka yadda suke bukata ba.
Kana a ganin masaniyar ilimin tattalin arziki ‘yar kasar Afirka ta Kudu, Annabel Bishop, cin zalin da kasar Amurka ke yi, zai sa kasashen Afirka gaggauta karkata ga abokan hulda dake kan hanyar tasowa wajen gudanar da ciniki.
Ban da haka, Leseko Makhetha, masanin ilimin tattalin arziki na kasar Lesotho, ya ce matsin lambar da kasar Amurka ta yi wa kasashen Afirka, za ta sa su kara kokarin gina yankin ciniki mai ‘yanci na nahiyar Afirka.
Yayin da a nata bangare, minista mai kula da masana’antu, ciniki da zuba jari ta kasar Najeriya, Jumoke Oduwole, ta ce matakin matsin lamba na Amurka ya sa Najeriya tabbatar da niyyar raya bangaren fitar da kayayyakin da ba su shafi danyen mai ba. A cewarta, Najeriya za ta yi kokarin inganta kayayyakinta, don neman sayar da su a karin kasuwannin kasashe daban daban.
Amurka na son toshe hanyar neman ci gaban tattalin arziki ta kasashen Afirka, da ta sauran kasashe masu tasowa na nahiyoyi daban daban. Sai dai ba za ta samu biyan bukata ba. Saboda matakin cin zalin ba zai haifar da komai ba, illa farkarwa, da dogaro da kai, da karfin zuci, da hadin kai, ga kasashe daban daban. Tabbas rinjayen kasashe, wadanda suke da adalci, za su ci nasara a karshe, a wannan gasar da ake gudanar da ita a duniya. (Bello Wang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp