Yunƙurin da ake yi na komawar Mohamed Salah ƙungiyar Besiktas ta Turkiyya ya rushe bayan ɓangarorin biyu sun kasa cimma matsaya kan sharuɗan kwantiragi.
Rahotanni sun ce tsohon ɗan wasan Liverpool ɗin ya buƙaci a ba shi kaso mai yawa daga kuɗin da za a samu ta sayar da rigunan ƙungiyar da sauran kayan kasuwanci.
Haka kuma, an samu saɓani kan kuɗin da wakilinsa zai karɓa, lamarin da ya sa tattaunawar ta tsaya.
Besiktas na fatan ɗaukar Salah ba tare da biyan kuɗin sauya sheƙa ba bayan barinsa Liverpool, har ma ta fara shirye-shiryen tallata zuwansa.
Rushewar yarjejeniyar babban koma baya ne ga Besiktas, wadda yanzu za ta fara neman wani ɗan wasan gaba kafin kasuwar saye da sayar da ‘yan wasa ta ƙare.
Salah mai shekara 34 a duniya har yanzu ba shi da ƙungiya.
Ana danganta shi da wasu ƙungiyoyi a gasar MLS ta Amurka da kuma Saudi Pro League, amma har yanzu babu wani tayin albashin da ya samu kan wanda yake nema.
Ana sa ran wakilansa za su ci gaba da tattaunawa da ƙungiyoyin da ke son ɗaukarsa domin ya samu sabuwar ƙungiya kafin fara kakar wasa mai zuwa.














