Tawagar ƙwallon ƙafa ta mata ta Nijeriya, Super Falcons, ta sha kashu da ci 3-2 a hannun Malawi a wasanta na farko na Gasar Kofin Nahiyar Afirka ta Mata (WAFCON 2026).
An buga wasan ne a filin wasa na Al Madina da ke birnin Rabat na ƙasar Morocco.
Wannan shi ne wasa na farko a Rukuni na C, wanda ya ƙunshi ƙasashen Malawi, Nijeriya, Masar da Zambia.
Bayan wannan rashin nasara, Nijeriya ta koma matsayi na uku a rukunin, yayin da Zambia ke jan ragama bayan ta doke Masar da ci 6-0.
A wasansu na gaba, Super Falcons za su kara da Zambia ranar Asabar.
Nijeriya na buƙatar samun nasara domin ƙara ƙarfin fatan tsallakewa zuwa mataki na gaba.
Ƙasashe biyu ne kawai daga kowanne rukuni za su samu gurbin zuwa zagaye na gaba na gasar.














