• English
  • Business News
Monday, October 27, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Cinikin Waje Na Kasar Sin Yana Inganta

by CGTN Hausa
2 years ago
Sin

A ‘yan kwanakin da suka gabata ne, jirgin kasan dakon kaya na farko tsakanin Sin da Turai, ya isa birnin Shanghai dauke da kayayyakin da za a baje a bikin baje kolin kasa da kasa na kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin CIIE karo na shida. Shi dai wannan jirgi ya taso ne daga birnin Duisburg na kasar Jamus dauke da TEU 70 na kwantenoni, wadanda darajarsu ta kai sama da kudin Euro miliyan 16. 

Wannan na nufin cewa, bikin CIIE karo na shida da aka dade ana jira yana kara karatowa, wanda hakan zai kara sanya sabbin kuzari ga bunkasuwar cinikin waje na kasar Sin.

  • Tinubu Ya Karya Doka Kan Nada Olukoyede A Shugabancin Hukumar EFCC –Kwararru
  • Zaben Kano: Ba Mu Yarda A Karya ‘Yancin Dimokuradiyya Ba – Kungiya

Alkaluman hukuma da aka fitar jiya Jumma’a na nuna cewa, darajar kayayyakin shige da fice na kasar Sin a rubu’i uku na farkon shekara, ta kai kudin Sin RMB yuan tiriliyan 30.8, wanda saurin karuwarta ya kusan yi daidai da na makamancin lokaci na shekarar bara. Tun daga farkon wannan shekara, farfadowar tattalin arzikin duniya ke fuskantar koma baya, kuma ci gaban kasuwancin duniya ya fuskanci matsi da dama. A cikin wannan yanayi, cinikayyar waje ta kasar Sin “mai inganci” ba ta zo cikin sauki ba.

A halin yanzu, “sabbin abubuwa guda uku” da motoci masu amfani da wutar lantarki, da batirin lithium da kuma na’urorin tattara hasken rana ke wakilta, sun zama sabbin alamun cinikin waje na kasar Sin.

A rubu’i uku na farkon shekarar bana, darajar sabbin kayayyakin uku da kasar Sin ta fitar, ta kai yuan biliyan 798.99, wanda ya karu da kashi 41.7 bisa 100 kan na shekarar bara, kuma yawansu da ke cikin jimillar kayayyakin da kasar Sin take fitarwa zuwa ketare, ya karu da kashi 1.3 cikin 100 kan na shekarar bara, har ya kai kashi 4.5 bisa 100. Hakan ya kara sanya sabon kuzari a cinikin waje na kasar Sin.

LABARAI MASU NASABA

Tunawa Da Dawowar Taiwan Kasar Sin Shekaru 80 Da Suka Wuce Yana Da Ma’ana Sosai

Kara Bude Kofofin Sin Zai Samar Da Karin Gajiya A Fannin Bunkasar Duniya

Yayin da tattalin arzikin kasar Sin ke ci gaba da farfadowa da ma inganta, baya ga aiwatar da wasu tsare-tsare da matakai yadda ya kamata, ana saran shigowa da fitar da kayayyaki za su ci gaba da karfafa kyakkyawan yanayin da ake ciki, da ci gaba da sanya kwanciyar hankali a harkokin cinikayyar duniya. (Ibrahim)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Tunawa Da Dawowar Taiwan Kasar Sin Shekaru 80 Da Suka Wuce Yana Da Ma’ana Sosai
Daga Birnin Sin

Tunawa Da Dawowar Taiwan Kasar Sin Shekaru 80 Da Suka Wuce Yana Da Ma’ana Sosai

October 26, 2025
Kara Bude Kofofin Sin Zai Samar Da Karin Gajiya A Fannin Bunkasar Duniya
Daga Birnin Sin

Kara Bude Kofofin Sin Zai Samar Da Karin Gajiya A Fannin Bunkasar Duniya

October 26, 2025
Ya Zuwa Satumban Bana Adadin Lantarki Da Sin Ta Samar Ya Karu Da Kaso 17.5%
Daga Birnin Sin

Ya Zuwa Satumban Bana Adadin Lantarki Da Sin Ta Samar Ya Karu Da Kaso 17.5%

October 26, 2025
Next Post
Wang Yi: Sin Tana Goyon Bayan Zaman Lafiya Da Adalci Da Lamirin Da Ya Shafi Dan Adam Kan Batun Falasdinu

Wang Yi: Sin Tana Goyon Bayan Zaman Lafiya Da Adalci Da Lamirin Da Ya Shafi Dan Adam Kan Batun Falasdinu

LABARAI MASU NASABA

Tunawa Da Dawowar Taiwan Kasar Sin Shekaru 80 Da Suka Wuce Yana Da Ma’ana Sosai

Tunawa Da Dawowar Taiwan Kasar Sin Shekaru 80 Da Suka Wuce Yana Da Ma’ana Sosai

October 26, 2025
Matatar Dangote Za Ta Faɗaɗa Ƙarfin Aiki Zuwa Ganga Miliyan 1.4 Kullum

Matatar Dangote Za Ta Faɗaɗa Ƙarfin Aiki Zuwa Ganga Miliyan 1.4 Kullum

October 26, 2025
Kara Bude Kofofin Sin Zai Samar Da Karin Gajiya A Fannin Bunkasar Duniya

Kara Bude Kofofin Sin Zai Samar Da Karin Gajiya A Fannin Bunkasar Duniya

October 26, 2025
“Ba Gudu Ba Ja Da Baya Game Da Tsarin “Call-up system” A NPA”

“Ba Gudu Ba Ja Da Baya Game Da Tsarin “Call-up system” A NPA”

October 26, 2025
Ya Zuwa Satumban Bana Adadin Lantarki Da Sin Ta Samar Ya Karu Da Kaso 17.5%

Ya Zuwa Satumban Bana Adadin Lantarki Da Sin Ta Samar Ya Karu Da Kaso 17.5%

October 26, 2025
Dalilin Da Suka Sa Hisbah Ta Dakatar Da Auren Ƴan TikTok A Kano

Dalilin Da Suka Sa Hisbah Ta Dakatar Da Auren Ƴan TikTok A Kano

October 26, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwarzon Ma’aikacin Gwamnati Na Shekarar 2025, Dakta Zacch Adedeji

October 26, 2025
An Yi Taron Tattaunawa Mai Taken “Shugabancin Duniya Da Samun Wadata Tare A Yankin Asiya Da Pasifik” A Beijing

An Yi Taron Tattaunawa Mai Taken “Shugabancin Duniya Da Samun Wadata Tare A Yankin Asiya Da Pasifik” A Beijing

October 26, 2025
Sin Da Amurka Sun Cimma Matsaya Dangane Da Tsare-Tsaren Warware Batutuwan Cinikayya Da Suke Mayar Da Hankali A Kai

Sin Da Amurka Sun Cimma Matsaya Dangane Da Tsare-Tsaren Warware Batutuwan Cinikayya Da Suke Mayar Da Hankali A Kai

October 26, 2025
Sharhi: Wannan Manufar Sin Za Ta Sa Kaimin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya

Sharhi: Wannan Manufar Sin Za Ta Sa Kaimin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya

October 26, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.