Gwamnan Jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya ya kaddamar da rabon kayan abinci da kayan noma don rage matsalolin tattalin arziki da ake fuskanta sakamakon cire tallafin man fetur ga al’ummar jihar.
Da ya ke jawabi a waje bikin rabon kayayyakin wadda aka gudanar a fadar Sarkin Yamaltu da ke Dadinkowa jiya, Gwamnan ya bayyana cewa kaddamar da rabon kayan tallafin wani gagarumin kokari ne na tallafawa fiye da mutane 450,000 da za su ci gajiya a fadin kananan hukumomi 11 na jihar.
“A kashi na farko da muka kaddamar a yau, za mu tallafawa mutane dubu 30,000 ne inda kowane mutum zai samu buhun shinkafa mai girman Kilogram biyar da katon din macaroni daya da buhunan taki biyu da lita biyu na maganin kashe kwari”.
“Abin da ya sa wannan shiri ya sha bambam da sauran shirye-shirye shi ne dabarar sanya kayan noma a cikin rabon kayan abinci, wannan shawarar tana da matukar tasiri duba da yadda kaso mai tsoka na al’ummar Jihar Gombe sun dogara ne da noma don gudanar da harkokin rayuwarsu.”
A cewarsa, ba da tallafin noman zai taimaka matuka wajen samar da isasshen abinci a lokacin kaka.
Da yake bayyana wajibcin cire tallafin man fetur, Gwamna Inuwa ya ce hakan wani mataki ne na tabbatar da dorewar tattalin arziki da ci gaba. Ya kara da cewa, an tsara tallafin ne bayan fahimtar irin kalubale daban-daban da magidanta ke fuskanta a Jihar Gombe sakamakon tabarbarewar tattalin arziki.
Baya ga rabon kayayyakin, Gwamna Inuwa ya ce, shirin tallafin yana kuma nuna tausayi da jajircewarsa ga jin dadin kowane dan Jihar Gombe.
Don haka ya bukaci al’ummar jihar su sanya dabi’un tausayi da hadin kai a cikin mu’amalarsu, tare da tallafawa mabukata.
Gwamnan ya yi kira ga jami’an rabon kayayyakin da ‘yan sa kai su gudanar da ayyukansu cikin gaskiya da rikon amana don tabbatar da gaskiya da adalci.
Gwamna Inuwa Yahaya ya tabbatarwa jama’a cewa gwamnatin sa tana kokarin ƙara samar da ayyukan yi ga al’umma don bunkasar harkokin ci gaba, da dakile kalubalen tattalin arzikin da jama’a ke fuskanta.
Shugaban kwamitin kula da rabon kayan abinci na jiha Abdullahi Haruna Abdullahi, ya tabbatarwa Gwamnan cewa kwamitin zai gudanar da aikinsa cikin tsantseni da tsoron Allah don amfanar al’umma.
Abdullahi wanda kuma shi ne Sakataren zartarwa na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Gombe SEMA, ya bayyana cewa an kafa wasu kananan kwamitoci a matakin kananan hukumomi da gundumomi don tabbatar da cewa kayayyakin sun kai ga marasa galihu a jihar.