Majalisar dokokin jihar Nasarawa ta kafa wani kwamiti da zai binciki yadda wasu jami’an gwamnatin jihar suka karkatar da kayan tallafin da aka kebe da nufin tallafawa masu karamin karfi da nufin rage musu radadin cire tallafin man fetur.
Shugaban majalisar, Ibrahim Balarabe Abdullahi ya yi alkawarin ne yayin zaman majalisar a ranar Talata cewa, doka za ta yi aiki kan duk wanda aka kama yana da hannu kan karkatar da kayan.
Jami’an Hukumar Yaki da yiwa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annuti (EFCC) sun kama wasu jami’an Hukumar ba da agajin Gaggawa ta Jihar (NSEMA) bisa zargin karkatar da kayan tallafin da aka shirya raba wa masu karamin karfi a jihar.
An zargi Jami’an NSEMA da sayar da kayan tallafin a kasuwar zamani da ke Lafia da kuma sauran kasuwanni.
Shugaban majalisar ya ce, majalisar dokokin jihar ta kafa kwamitin mutum bakwai da zai binciki zargin karkatar da kayan tallafin.
Majalisar ta kafa kwamitin ne biyo bayan kudirin da Hon. Musa Ibrahim Abubakar (NNPP- Doma ta Kudu) ya kawo, inda ya ce, ya dace Majalisar ta binciki wadanda ake zargi da aikata wannan mummunan laifin.