Gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammad ya kaddamar da rabon buhun shinkafa guda 88,889 mai nauyin kilo 25 da sauran nau’ikan tallafi daban-daban domin raba wa masu kananan karfi da cire tallafin man fetur ya jefa cikin mawuyaciyar rayuwa a jihar.
An kaddamar da rabon ne a ranar Asabar a filin wasanni na Abubakar Tafawa Balewa da ke birnin jihar, Gwamna Bala ya gargadi dukkanin jami’an da aka bai wa alhakin rabon da su tabbatar da sun rike amana da yin rabon bisa yadda aka tsara domin tabbatar da kwalliya ta biya kudin sabulu.
Sarkin Bauchi, Dakta Rilwanu Sulaiman Adamu, shi ne shugaban babban kwamitin rabon, yayin da mataimakin gwamnan jihar, Muhammad Auwal Jatau ya kasance shugaban kwamitin ayyuka da tsara rabon tallafin domin ganin ya shiga lunguna da sako na jihar.
Gwamnan ya kuma sanar da cewa, a karkashin rabon kudin tallafin da aka tsara, za a kashe Naira Miliyan 800 wajen biyan kudaden fansho na jiha da na kananan hukumomi inda kuma gwamnatin jihar za ta kara naira biliyan uku wajen biyan kudaden giratuti na jiha da na kananan hukumomin a kokarin gwamnatin na tausaya wa jama’a kan halin da aka shiga na matsi sakamakon cire tallafin mai din.
Dukka a cikin tsarin tallafin, gwamna Bala Muhammad, ya sanar da cewa naira miliyan N680,000,000 za a kashe ta ne wajen biyan kudin hutu ga ma’aikata, wato (LTG), sai kuma aka ware naira miliyan N110 domin tallafa wa Mata da Matasa da nufin su tsayu da kafafunsu.
Kazalika, an ware Naira Miliyan N300,000,000 da za a rabar wa marasa karfi ta cikin shirin ‘conditional cash transfer’ (CCT), bugu da kari, za a dauki ma’aikatan sa-kai har su 1,000 a cibiyoyin kiwon lafiya da za a ke biyansu naira N10,000 kowace wata na tsawon watanni shida da hakan zai lakume Naira Miliyan N60,000,000.
Ya cigaba da cewa, “Mutane masu fama da nakasa ta musamman za su samu naira miliyan 10, ma’aikatan da ke shara don tsaftace muhallin cikin gari za su samu naira miliyan N37, jami’an tsaron sa kai na Zabgai za a basu naira miliyan N42, jami’an tsaron Spider kuma naira miliyan 21.”
Dangane da tsarin rabon shinkafar kuwa, gwamna Bala ya ce, kungiyoyin fararen hula, kungiyoyin addinai na musulmai da kirista, ‘yan banga, tsoffin sojoji, masu ruwa da tsaki, talakawa da marasa galihu ne za su ci gajiyar shirin.
Kazalika, ya bayyana cewar tun kafin wannan ranar a kokarinsa na ganin an samar da sauki ga al’umma tun bayan cire tallafin mai din, gwamnatinsa ta sayo motocin sufuri na zamani guda 30 kana ta zuba su cikin sha’anin sufuri a rahusa mai sauki domin taimaka wa jama’a.
Tun da farko a nasa jawabin, shugaban kwamitin tsare-tsaren rabon tallafin wanda shi ne mataimakin gwamnan jihar, Hon. Auwal Mohammed Jatau, ya fara ne da jinjina wa kokakin gwamna Bala Muhammad wajen tsayuwar daka domin nema wa al’ummarsa sauyin rayuwa.
Ya yi tilawar cewa gwamna Bala tun a farkon mulkinsa ya kaddamar da wani shirin samar da abubuwan dogaro da kai ga al’ummar jihar ta cikin (KEEP) da ya lakume sama da biliyan 3 wanda a cewarsa an ga natijar hakan domin da dama sun fita daga cikin matsalar talauci.
Babban shugaban kwamitin rabon tallafi, Sarkin Bauchi, Dakta Rilwanu Sulaiman Adamu, ya nuna farin cikinsa da ganin ranar da za a kaddamar da fara rabon, yana mai cewa tabbas hakan zai rage wa jama’a matsatsin da ake ciki a halin yanzu.
Sarkin ya yaba wa Gwamna Bala Muhammad bisa kokarinsa wajen samar da tallafi da agaji ga al’ummar jihar, ya nuna cewa zai sanya ido wajen ganin al’umma sun mari tallafin da aka ware dominsu.