Alkaluman da kungiyar masana’antun sarrafa karfe ta kasar Sin wato CISA ta fitar na cewa, tsakanin watan Janairu zuwa watan Agustan bana, harkokin masana’antun sarrafa karfe suna tafiya cikin yanayin mai karko. Yawan karafa da aka sarrafa a duk fadin kasar Sin ya kai ton miliyan 909, adadin da ya karu da kaso 6.3 bisa dari idan aka kwatanta da na makamancin lokacin bara.
Kwararru na ganin cewa, bukatun karfe na sauyawa cikin kasar Sin sakamakon kwaskwarimar da aka yi kan tsarin masana’antun sarrafa karfe. Bukatun kayan karfe da ake amfani da su domin kera motoci na ci gaba da karuwa, kuma, bukatunsu a fannin gina ababen more rayuwa na samar da wutar lantarki da makamashi daga karfin iska da hasken rana su ma suna karuwa. A sa’i daya kuma, bukatun karfe a fannin gina jiragen ruwa da na’urorin wutar lantarki su ma suna karuwa. Shi ya sa, tafiyar da harkokin masana’antun sarrafa karfe cikin watanni 8 na farkon bana suka gudana yadda ya kamata.
- Ra’ayin Gina Al’umma Mai Kyakkyawar Makoma Ta Bai Daya Na Tattaro Karfin Sauya Duniya
- Al’adun Kasar Sin Na Da Tushen Neman Zaman Lafiya Tun Lokacin Da
Har ila yau, a watan Agustan bana, ma’aikatar harkokin masana’antu da sadarwa ta kasar Sin da kwamitin yin kwaskwarima da raya kasa da wasu hukumomi gaba daya guda 7, sun yi hadin gwiwa wajen gabatar da “shirin raya masana’antun sarrafa karfe cikin yanayin mai karko”, shirin da ya bayyana burin neman karuwar masana’antun sarrafa karfe a bana, wanda adadin karuwarsu zai kai kaso 3.5 bisa dari. Kana, an gabatar da manyan matakai guda hudu, da suka hada da yin kirkire-kirkire kan fasahohin da abin ya shafa, kara ingancin kayan karfe, da kara karfin sarrafa karfe, da kuma kyautata karfin manyan kamfanonin dake kan gaba a wannan fanni.
Wasu masana na ganin cewa, matakai da manufofin da aka fidda, za su ba da gudummawa wajen tabbatar da karuwar masana’antun sarrafa karfe cikin yanayin zaman karko. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)