Ciwon Mara lokacin al’ada matsala ce da take damun yawancin mata, musamman ma wadanda ke fama da shafar aljanu ko matsalolin jikin ciki.
Hadin gargajiya don ciwon ciki saboda Aljanu:
Abubuwan da za ku tanada:
Garin zogale cokali 4, Bakin ridi cokali 8, Dakakken barkono rabin cokali, Zuma mai kyau kofi 3
- Yadda Wasu Mata Ke Gallaza Wa ‘Ya’yansu Domin Bakanta Wa Mazajensu
- Ƙungiyar Fulani Makiyaya Ta Nuna Damuwarta Na Ɓacewar Mataimakin Shugabanta
Yadda ake amfani da shi:
A gauraya kayan hadi cikin zumar, a rika sha cokali 3 da safe bayan karyawa da kuma da dare kafin kwanciya. A fara amfani da wannan hadi kafin zuwan al’ada, sannan a ci gaba har ciwon ya lafa, da izinin Allah.
Ciwin Ciki na mata mai zafi
Hadi mai matukar karfi:
Garin hulba cokali 7, Garin habbatussauda (habbur rashad) cokali 7, Man zaitun cokali 10
Yadda ake amfani da shi:
A gauraya su wuri guda. A rika diban cokali 2, a tafasa, sai a tace, sannan a zuba zuma kadan a ciki sai a sha. A fara amfani da wannan hadin kwana 5 kafin zuwan al’ada, a ci gaba har lokacin al’adar. Wannan zai kara lafiya da ni’ima a jiki.
Wani Hadin:
Tsamiya, Habbatussauda, Zuma:
Yadda ake amfani da shi:
A tafasa tsamiya da habbatussauda, a tace, sannan a zuba zuma a ciki. A rinka sha sau biyu a rana. Wannan shima yana da tasiri sosai wajen saukar da zafi da busar da radadin ciwo.
Wani Hadin:
Hadin Citta da Kanafari:
Citta (zanyen ko garinta), Kanunfari, Zuma
A tafasa citta da kanunfari, a tace ruwan, a zuba zuma a sha, yana saukaka ciwon mara musamman ga wadanda suke da matsalar kumburin mahaifa.
Ganyen gwanda da Lemo:
ganyen gwanda rabi, Ruwan lemon tsami
A markada ganyen gwanda da ruwan lemon tsami, a tace a sha. Yana taimakawa wajen tsaftace mahaifa da rage radadin mara. Ko kuma a dafa.
Tsarki da Ganyen Magarya:
A tafasa ganyen magarya, a zauna ciki (wankan dumi) na mintuna 15, musamman idan al’ada ta zo da zafi. Wannan na rage jin radadi da kwantar da mahaifa.














