Ciyarwa tana da girman matsayi da lada a wurin Allah mai tarin yawa. Allah Ya ce: Waɗanda suke ciyar da dukiyoyinsu dare da rana a fili da ɓoye, to, suna da ladansu a wurin Ubangijinsu. Kuma babu tsoro a tare da su, kuma ba za su yi bakin ciki ba” Sūratul Baƙara aya ta 274.
Duk wanda ya yi sadaƙa, Allah Zai karɓi sadaƙar kuma ya riƙa kula da ita komai ƙanƙantarta har ta zama ƙatuwa. Annabi sallallahu alaihi wa alihi wa sallam ya ce: “Duk wanda ya yi sadaƙa daidai da tsagin dabino, to, lalle Allah zai karɓa da damansa, sa’an nan ya raine ta ya mayar da ita kamar yadda ɗayanku yake rainon ɗan dokinsa, har ta zama kamar ƙaton dutse” Bukhari [#1410, da #7430] da Muslim [#1014].
Duk wanda ya yi sadaƙa a fili ko a boye, to, Allah yana sane da abin da ya ciyar. Kuma hakan zai sanya a kankare masa zunubansa da ya aikata. Allah yana cewa: “Idan za ku bayyanar da sadakokinku a fili, to, madalla da yin hakan, idan kuma kuka boye sadakar kuka bayar da ita ga talakawa, to, hakan shi ya fi alheri a gare ku, kuma zai kankare muku kusakurenku, Allah kuma masani ne dangane da abin da kuke aikatawa” Sūratul Baƙara aya ta 271.
Duk wanda ya ciyar da bayin Allah, to , Allah zai ciyar da shi. Manzon Allah (S.A.W) ya ce:” Allah ya ce: Ya kai ɗan’adam! Ka ciyar zan ciyar da kai. Shin ba ku ga abin da ya ciyar ba tun lokacin da ya halicci sama da ƙasa amma bai tauye abin da yake hannunsa ba, kuma Al-arahinsa yana kan ruwa…” Bukhari [#4684] da Muslim [#993].