Kamfanin gungun gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin CMG, da lardin Jiangsu na kasar, sun sanya hannu kan yarjejeniyar hadin gwiwa ta tallata tamburar hajojin lardin a jiya Laraba 25 ga watan nan.
Yayin bikin sanya hannun da aka gudanar a birnin Nanjing na lardin, babban daraktan CMG Shen Haixiong, ya gabatar da jawabi, inda ya ce a matsayin CMG ta kafa mafi girma a duniya, kuma mafi dora muhimmanci ga harkokin kasuwanci, kana cikakkiyar kafar watsa shirye shirye ta kasa da kasa, tsarin CMG na tallata tamburar hajoji, ya yayata hajojin kasar Sin masu tarin yawa, ta yadda suka zamo fitattu a cikin gida da waje, wanda hakan ya tabbatar da matsayi, da karfin kafar tsakanin ra’ayoyin al’ummun kasa da kasa. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp