Jiya Alhamis 23 ga wata ne, sashin CGTN na babban rukunin gidan rediyo da talabijin na kasar Sin ko kuma CMG a takaice, ya hada kai tare da manyan kafafen yada labaran wasu kasashen Afirka biyar, ciki har da gidajen talabijin na kasashen Mauritius, da Rwanda da Gabon, gami da gidan talabijin na MATV dake Madagascar, da wani gidan talabijin dake Jamhuriyar Benin, inda suka kaddamar da wani shirin TV tare da ake kira “More ci gaba tare”.
A ranar 23 ga watan Maris din shekara ta 2013, a kasar Rasha, karo na farko shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya bayyanawa duk fadin duniya wani muhimmin ra’ayi, wato gina al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya, al’amarin da ya jawo hankalin kasa da kasa, tare da shiga cikin zukatan al’umma sosai.
Shirin TVn mai suna “More ci gaba tare” zai maida hankali kan wasu muhimman batutuwa, ciki har da kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha, da samar da ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba, da farfado yankunan karkara, da karfafa hadin-kan Sin da Afirka, a wani kokari na yi wa masu kallo na kasashen Afirka karin haske, dangane da ainihin ma’anar “zamanantarwa irin ta kasar Sin”, da ra’ayin gina al’ummomin Sin da Afirka masu kyakkyawar makoma ta bai daya, gami da bayyana musu dabarun kasar Sin na samar da ci gaba. (Murtala Zhang)