A yau Laraba ne rukunin yada labarai na kasar Sin (CMG) ya fitar da manyan labaran kasa da kasa guda 10 na shekarar 2023, a wani taron manema labarai da aka gudanar a cibiyar yada labarai da ke nan Beijing.
Ga kanun wadannan labaran a kasa
1. Diflomasiyyar shugabancin kasar Sin ya sanya kwanciyar hankali a cikin duniya mai cike da tashin hankali.
2. Kasar Sin ta sanar da manyan matakai guda takwas don zamanantar da duniya yayin da ake cika shekaru 10 da gabatar da shawarar BRI
3. Sabon rikici ya barke tsakanin Hamas da Isra’ila
4. Shiga tsakanin da kasar Sin ta yi wajen sasanta Saudiyya da Iran ya samu yabo a Gabas ta tsakiya
5. Tattalin arzikin duniya na farfadowa cikin wahala, inda kasar Sin ta kasance wuri mai haske
6. Rikicin Rasha da Ukraine ya kai makura
7. SCO da BRICS sun fadada, Tarayyar Afirka ta shiga G20
8. El Nino ya haifar da matsanancin yanayi akai-akai a wannan shekarar da ta zama ‘shekara mafi zafi’ a tarihi
9. An samu karuwar ababe masu amfani da fasahar AI a 2023, yayin da yadda za a kula da su ya zama abin damuwa a duniya
10. An tsige Kevin McCarthy a matsayin kakakin majalisar wakilan Amurka