A ranar 12 ga watan Oktoba, agogon wurin, babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin na CMG ya gudanar da bikin kaddamar da bikin baje kolin “Hanyar samun wayewar kai”, a tsohon wurin adana kayan tarihi na Royal Mint da ke birnin London na kasar Birtaniya.
Shugaban CMG Shen Haixiong, ya bayyana a cikin wani jawabi ta kafar bidiyo cewa, bikin baje kolin “Hanyar samun wayewar kai” da za a gudanar a sassa daban daban na duniya, ya kai ga gano tushen “wayewar kan kasar Sin” ta hanyar batun “Mene ne wayewar kai”, wannan ya kai mu ga nasarar gano al’adun gargajiyar kasar Sin, bayan baje kolin al’adu na kasar Sin.
Sarafa Tunji Isola, babban jami’in ofishin jakadancin Najeriya a kasar Birtaniya, ya bayyana a yayin wata hira da ya yi da CMG cewa, a ‘yan shekarun nan, kasashen Najeriya da Sin sun samu sakamako mai kyau a fannin hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya, kuma ayyukan musayar al’adu na iya taimakawa wajen kara fahimta da mutunta juna, da kuma rage rashin fahimtar juna da bambance-bambance, da fatan Najeriya da Sin za su zurfafa mu’amalar jama’a da ta al’adu.(Ibrahim)