A yayin ziyarar aiki da shugaban kasar Sin Xi Jinping zai kai kasar Rasha, da kuma halartar bikin cika shekaru 80 da samun nasarar yakin kiyaye kasa na Tarayyar Soviet, CMG ya kaddamar da nuna fina-finai da shirye-shiryen talabijin na kasar Sin masu inganci a kasar Rasha a birnin Moscow. An kuma watsa ayyuka fiye da goma da CMG ya shirya a muhimman kafafen yada labaru na kasar Rasha, irinsu “Dangantakar al’adu ta Xi Jinping”, da “Fahimtar kasar Sin: Hanya ta musamman don samun zamanantarwa”.
Shen Haixiong, shugaban CMG, ya gabatar da wani jawabi ta kafar bidiyo. Ya ce, bana ita ce “shekarar al’adun Sin da Rasha”, kuma CMG da kafofin watsa labaru na kasar Rasha sun gudanar da wannan baje kolin tare, wannan wani mataki ne na hakika na aiwatar da matsayin da shugabannin kasashen biyu suka cimma, da karfafa mu’amalar al’adu tsakanin kasashen biyu, da kuma karfafa tushen ra’ayin jama’a na sada zumunta tsakanin kasashen.
Ya kara da cewa, ta hanyar shirye-shirye masu inganci irin su “Dangantakar al’adu ta Xi Jinping”, da “Fahimtar kasar Sin: Hanya ta musamman don samun zamanantarwa”, da “Labarina a Sin”, da kuma “Jituwar mabanbantan sassa”, dimbin masu sauraron harshen Rasha za su kara fahimtar sabbin ayyukan zamanantarwa irin ta Sin, kuma za su ji karfin kuzarin kasar Sin a sabon zamani, da kuma kyawun al’adun Sin na musamman. (Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp