Ranar 26 ga watan nan, babban rukunin gidajen rediyo da talibijin na kasar Sin (CMG) ya kaddamar da wasu ayyukan samun ci gaba mai inganci a birnin Shanghai. Shugaban CMG Shen Haixiong da shugaban sashen harkokin yayyata birnin Shanghai Zhao Jiaming, sun halarci bikin kaddamar da ayyukan tare da gane wa idanunsu yadda ofishin CMG a Shanghai, da jami’ar koyon harsunan waje ta Shanghai, da kamfanin fina-finai na Shanghai suka daddale yarjejeniyar hadin kai bisa manyan tsare-tsare.
Wadannan ayyukan sun hada da na hada-hadar kudi da kuma shirye-shiryen fina-finai da talibijin da za a nuna a kasa da kasa, a kokarin kara azamar gudanar da mu’amala tsakanin mabambantan al’adu. (Tasallah Yuan)














