Cristiano Ronaldo ya ki amincewa da damar sake komawa matsayinsa na dan wasan kwallon kafa da ya fi karbar albashi a duniya, bayan da rahotanni suka ce kungiyar kwallon kafa ta Al-Hilal da ke Saudiya, ta yi masa tayin kwantiragin shekaru biyu da ya kai Yuro miliyan 242.
Duk da cewa jaridar wasanni ta MARCA da ke kasar Spain, ta tabbatar da rahotan zawarcin dan wasan bayan bullarsa a Portugal, Ronaldo a halin yanzu ya amince da ci gaba da zama a Manchester United.
- Ministan Najeriya Ya Yi Maraba Da Kamfanonin Sin Da Su Zuba Jari A Kasar
- Launukan Kawata Falo Masu Ban Sha’awa (4)
Kaftin din tawagar ‘yan wasan kasar Portugal, ya yi kokarin barin Old Trafford a wannan kakar wasannin don samun kungiyar da ke buga gasar zakarun Turai, musamman yadda ba ya jin dadin zama a Manchester United, amma duk da haka ya fi son ci gaba da zama a Turai.
A watan Yuli da kuma Agusta, an danganta Cristiano da komawa kungiyoyi irin su Atletico Madrid da Marseille da Sporting Clube de Portugal dama Napoli.
Kungiyar ta Al-Hilal ta amince ta biya Ronaldo Yuro miliyan 121 duk shekara, amma dan wasan ba ya son barin Turai, duk da rashin buga gasar zakarun Turai a kakar wasa ta bana.