A ƙalla mutane 13 ne suka rasa rayukansu sakamakon ɓarkewar cutar amai da gudawa (cholera) a ƙananan hukumomi shida na jihar Neja tun daga watan Janairu na shekarar 2025.
Binciken da LEADERSHIP ta gudanar ya nuna cewa an tabbatar da kamuwar mutane 236 da cutar a lokacin da ta ɓarke, inda daga cikinsu aka rasa mutane 13.
- Sojoji Sun Kama Mutane 50 Masu Fasa-ƙwaurin Mai Da Lalata Haramtattun Matatun Mai A Neja-Delta
- Neja: Cikin Wata 10 Ibtila’i Ya Lakume Rayuka Sama Da 400 – NSMA
Wasu daga cikin waɗanda suka kamu da cutar na ci gaba da samun kulawar likitoci a cibiyoyin lafiya daban-daban.
Al’ummomin da cutar ta shafa sun haɗa da ƙananan hukumomin Chanchaga, Bosso, Shiroro, Magama, Bida da kuma Munya.
A makon da ya gabata a ma’aikatun lafiya a matakin farko da na sakandare suka fara haɗin gwuiwar fuskantar matsalar ta Kwalara a faɗin jihar, inda suka bayyana cewa jimillar mutanen da suka rasa rayukansu tun watan Janairu ya kai 26.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp