Cutar kwalara ta yi sanadiyar mutuwar mutane hudu a karamar hukumar Bokkos na jihar Plateau, yayin da wasu da dama suka shiga asibiti don jinya. Majiyarmu ta samu rahoton cewa an tura wasu marasa lafiya zuwa wasu cibiyoyin kiwon lafiya da asibitun yankin domin kulawa.
Shugaban karamar hukumar Bokkos, Hon. Amalau Samuel, ya tabbatar da lamarin ga manemanmu a ranar Litinin, inda ya bayyana cewa an samu bullar cutar a yankunan Hurti Community, Bokkos West, Bokkos Central da Mangol.
- Rikicin Filato Ya Sa Makiyaya Yin Asarar Naira Miliyan 300 Cikin Wata 2
- Sojoji Sun Cafke Dillalan Sayar Da Bindigu A Filato
Ya ce sashin kula da lafiya a matakin farkokokarin kai agaji don magance matsalar, yayin da wasu marasa lafiya suka warke aka sallame su.
“Mun samu bullar cutar kwalara a wasu mutane da ke Bokkos. Wadanda suka rasu sun kai mutane hudu, wasu kuma suna jinya yanzu. Muna kira ga al’umma su kiyaye tsafta, su wanke hannu akai-akai, su wanke ‘ya’yan itace kafin su ci, su kuma sha ruwa mai tsafta,” in ji shi.
Shugaban ya kuma bukaci jama’a da su kai rahoton alamun cutar zuwa cibiyoyin kiwon lafiya mafi kusa da su ko kuma asibitin Cottage na Bokkos.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp