Kungiyar manoman Tumatir reshen jihar kano TOGAN ta bayyana cewa, cutar da ke yiwa Tumatir Illa ta sake afkawa a wasu gonakan manona da ke a cikin jihar.
Shugaban kungiyar reshen jihar Alhaji Sani Danladi Yadakwari ne ya bayyana hakan a hirarsa da manema labarai inda ya ce, sun zargin cutar ta Tuta ce da ke lalata Tumatir.
A cewar shugaban, kungiyar ta dauki kwararan matakai domin mu kare yaduwar cutar zuwa sauran gonakan manoman na Tumatir da ke a daukacin fadin jihar.
Shugaban ya ci gaba da cewa, idan ba yi hankali ba, a kakar noman sa ta bana za a iya samun karancin sa.
” Mun dauki kwararan matakai domin mu kare yaduwar cutar zuwa sauran gonakan manoman na Tumatir da ke a daukacin fadin jihar.”
Yadakwari ya bayyana cewa, mun lura da bullar wannan cutar ta tuta a wasu kananan hukumin Jihar kamar a Garun Mallam da Bunkure da kuma a wasu gurare da ke a cikin jihar.
Shugaban ya bayyana cewa, a kungiyance mun yi iya namu kokarin, inda muka rubuta wasiku domin sanar da ma’aikatar aikin noma ta jihar.
Ya sanar da cewa, wannan cutar ba karamar koma baya za ta janyo wa manoman na Tumatir da ke a cikin jihar ba.
Shugaban ya bayyana cewa, ya zama wajibi gwamnatin jihar ta kawo mana daukin gaggawa domin gudun kar manoman na Tumatir da ke a cikin jihar su tabka asara da kuma magance karancin sa a daukacin fadin jihar.
” Ya zama wajibi gwamnatin jihar ta kawo mana daukin gaggawa domin gudun kar manoman na Tumatir da ke a cikin jihar su tabka asara da kuma magance karancin sa a daukacin fadin jihar. ”
Bisa wani bincike da aka gudanar ya nuna cewa, cutar na tafiya ne sai kuma ta sake dawo wa, tum bayan lokacin da ta bulla a shekarar 2016.
” Ya zama wajibi gwamnatin jihar ta kawo mana daukin gaggawa domin gudun kar manoman na Tumatir da ke a cikin jihar su tabka asara da kuma magance karancin sa a daukacin fadin jihar. ”
Da aka tuntubi daraktan ma’aikatar aikin noma da raya karkara na tarayya da ke a cikin jihar Alhaji Baba Gana akan maganar ya bayyana cewa, kungiyar ta tuntubi ma’aikatar kan maganar kuma da zarar sun samu cikakkun bayanai za su dauki matakan da suka kamata akan matsalar, musamman domin a dakile yaduwar cutar zuwa sauran gonakan manoman na noma Tumatir da ke a cikin jihar.
“ Kungiyar ta tuntubi ma’aikatar kan maganar kuma da zarar sun samu cikakkun bayanai za su dauki matakan da suka kamata akan matsalar, musamman domin a dakile yaduwar cutar zuwa sauran gonakan manoman na noma Tumatir da ke a cikin jihar. ”
A wata sabuwa kuwa, wasu daga cikin masana a fannin noman masara a kasar nan, sun sanar da cewa, kokarin manoman ta a kasar nan bai kai ga yanda za’a iya yayatawa ba ba, domin kuwa a ganin su da ace ana aiwatar da abubuwan da ake fada a baki to da yanzu kasar ta tara da takwarorinta da suka yi mata nisa wajen noman rani irin su Masar.
A cewar masanan, Nijeriya za ta iya shiga gaban Masar wajen noman tumatir, saboda idan ka duba , kashi saba’in cikin dari na kasar Masar Sahara ce, inda kuma Nijeriya Allah ya albarkace ta da kasar noma mai inganci, amma bama bin hanyoyin da suka dace.
Masana dai na da ra’ayin cewa da hukumomi a Nijeriya har yanzu ba su fargaba ganin yadda suke yiwa fannin na noma rikon Sakanaira Kashi.
Duk da cewa kasar na daga manyan masu noman tumatur a duniya, har yanzu kasar na shigo da Tumatur daga kasashen waje domin amfanin ‘yan kasar.
Alhaji Abdulrahim Ali wani manomi a karamar hukumar kura a jihar Kano ya sanar da cewa, suna noman tumatir, amma idan masu siya basu zoba, dole ne mu dauka su kai kasuwa mu siyar da araha domin kada ya lallace.
Shi kuwa Malam Dan Lami Umar sakatare na Kungiyar masu sai da kayan gwari ta jihar Kano ya sanar da cewa, wannan shine lokacin da ake asara, saboda ko ta ina akwai kayan miya.
Ya kara da cewa, wani manomin idan kaje gonarsa za ka samu kwando guda dubu biyu zuwa dari biyar ko kuma dari, inda ya kara da cewa, ko kuma idan an kawowa kasuwa, da gwamnatin tana talafawa ba zaa dinga samun irin wannan yanayi ba.
Kwamishinan noma na jihar Kano Alhaji Musa Sulaiman Shanono ya ce gwamnatin ta na iyakacin kokarinta domin magance wanan matsala.
Alhaji Musa ya kara da cewa, gwamnati ta na sane kuma ta damu kwarai, gwamnatin kano ta kulla yarjejeniya domin samarda kamfanin da zai dinga sarrafa tumatir domin taimakawa manoma.